Abdullahi Muhammad Sheka" />

Ganduje Ya Yi Ta’aziyyar Marigayi Alfa Wali Da Abdulhamid Hassan

Abubakar Zakari

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da Ta’aziyya ga iyalan marigayi tsohon Ministan Noma Alhaji Alfa Wali Wanda ya rigamu gidan gaskiya kwanan nan. Kamar yadda Daraktan yada labaran Mataimakin Gwamnan Hassan Musa Fagge ya shaidawa LEADERSHIP A Yau.

Wali ya kuma taba zama sakataren Gwamnatin tsohuwar Jihar Kano kuma tsohon babban sakataren Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya daban daban.
Gwamnan wanda mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya wakilta, wanda ya Jagoranci kai Ta’aziyyar gidajen mamatan biyu, Gwamnan ya ce, “mun yi rashin ‘yan kishin kasa wadanda suka gudanar da ayyukansu yadda ya kamata kuma suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen ciyar da kasarnan Jihar Kano gaba. Mu na rokon Allah ya bai wa iyalansu juriyar wannan babban rashi.”
Gwamnan wanda mataimakinsa ya kara wakilta a wajen jana’izar Marigayi Alhaji Abdulhamid Hassan, wanda tsohon Kwamishina ne a Ma’aikatar ilimi ta tsohuwar Jihar Kano. Marigayin gogaggen masanin harkar ilimi ya mutu a ranar Talata bayan gajeruwar rashin lafiya.
A cewar Ganduje, “Marigayi Alhaji Abdulhamid Hassan ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen cigaban ilimi a tsohuwar Jihar Kano, kuma ba za’a taba mantawa dashi ba. Za mu cigaba da yi masi addu’ar fatan Allah ya ba su aljanna madaukakiya.”

Exit mobile version