Ganduje Ya Zabi Sarkin Kano Don Kula Da Mukabalar Malaman Kano Da Sheikh Abdujabbar

Abduljabbar

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar, ya zabi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, don kula da muhawarar za a gudanar tsakanin Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara da wasu malamai a Kano.

Gwamnan, a wata hira da Muryar Amurka ya ce, za a yi muhawarar ne a Fadar Sarkin na Kano, saboda yanayin batun addinin da za a tattauna.

“Mun amince cewa za a yi muhawarar, saboda Sheikh Abduljabar ya nemi a yi muhawarar, kuma bayan ya tattauna batun cigaban tare da malamai a jihar, duk sun amince.”

Ganduje ya ce, a yanzu haka, Gwamnatin Jihar Kano na jiran malaman dake jihar su gama shirya wa muhawarar, sannan su amince da ranar da za a yi muhawarar.

Ya ce Gwamnatin Jiha ta hana Sheikh Abduljabar dake cikin rikicin ne, saboda kalaman da ya yi na zargin “rashin mutunta Annabin Musulunci,” da kuma kalaman da ka iya haifar da rudani ba kawai a jihar ba, har ma da kasar bakidaya.

Gwamnan ya kara kuma da cewa, ce, makomar masallacin malamin da kuma cigaba da wa’azinsa ya dogara ne kacokam kan sakamakon rahoton binciken tsaro.

Exit mobile version