Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a ranar Laraba ya gana da Sarakuna biyar na Masarautar Kano wadanda suka hada da Sarkin Kano, Bichi, Rano, Karaye da Gaya a wani bangare na kokarin kara kaimin yakar annobar Korona a jiko na biyu. Kamar babban Daraktan yada labaran gwamnan Abba Anwar Ya shaida wa LEADERSHIP A Yau Juma’a da yammacin Laraba.
Ganduje ya kuma tabbatar wa da Sarakunan kokarin Gwamnatin Jihar Kano na yaki da annobar a zagaye na Biyu.
Ya ce, “Babu shakka annobar Korona ta sake dawowa, hakazalika mu ma za mu sake dawowa kan yaki da annobar ba tare da gajiya ba. Kamar yadda ake cewa duk abin da ya tsananta dole a ci gaba da kara himmatuwa akan lamarin. Saboda Haka za mu kara kaimi a ko da yaushe, har sai mun tabbatar da dakile yaduwar annobar Korona baki daya.”
“Mun fara wannan shirin da ku Sarakuna, kasancewar ku ne kuka fi kusanci da al’amuran tun daga fari.”
“Ku je ku ci gaba da aiki tare da dagatai, masu unguwanni, malamai da sauran shugabannin al’umma, domin ganin an magance annobar Karo na biyu. A hada hannu wajen aiwatar da wannan aiki.”
“Muna farin ciki da irin gudunmawar da sauran shugabannin sassa daban-daban ke bayarwa. Tun zagayen farko na annobar ta Korona, mun san kun ba da gagarumar gudunmawa ga al’ummar ku. Wannan abin ayaba ne kwarai da gaske.,” In ji shi.
“Jihar Kano na fuskantar karuwar kamuwa da annobar Korona. Tun daga 14 ga watan Nuwamban shekara ta 2020 zuwa 17 ga watan Janairun Shekara ta 2021 an samu karin mutane 827 da suka kamu da annobar, wanda hakan ya kawo jimlar mutane 2,636 da suka kamu da Korona a Kano.”
Shugaban Kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar Korona, Sabitu Shanono ya ce, “a makon da ya gabata an samu karin wadanda suka kamu da cutar ta Korona zuwa kaso 12.7% idan aka kwatanta da kaso 4.2% na wadanda gwajin ya nuna ba sa dauke da Cutar. Jimlar wadanda ke kwance a wurare kilacewa ko asibitodi sun kai adadin mutane 289,”
“An samu adadin wadanda suka mutu da suka Kai mutum 17 tsakanin watan disambar da watan Janairu, halin da aka rabu da samun irin sa tun 15 ga watan Yulin 2020.”
‘Wasu daga cikin kalubalen da za a fuskanta a zagaye na Biyu na annobar ta Korona, sun hada da rashin kiyaye ka’idojin kariya, karancin aminta da wanzuwar cutar, da kuma rashin bayar da hadin Kai wajen halartar wuraren killace mutanen ko amfani da kayan wuraren killacewa,” in ji Shanono.
Da yake gabatar da jawabinsa, shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kano, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tabbatarwa da Gwamna cikakken goyon bayan dukkan Sarakuna domin samun nasarar yakin da annobar Korona, ganin yadda annobar ta sake kunno kai.