Abdullahi Muhammad Sheka">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Ganduje Zai Mayar Da Kamfanin Jarifar Triumph Kasuwar Canjin Kudi

by Abdullahi Muhammad Sheka
August 1, 2020
in LABARAI
2 min read
Ganduje Ya Jinjina Wa Gwamnatin Tarayya Kan Shimfida Bututun Iskar Gas
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yana duba wata shawara da wani kamfani mai zaman kansa ya bayar ta mayar da harabar Kamfanin Jaridar Triumph zuwa kasuwar ccanjin dudaden kasashen Waje.
Wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hukda da jama’a na fadar gwamnatin jihar Kano, Aminu Kabir Yassar ya ayyana ranar Laraba ta ce Gwamna Ganduje yana kuma duba yiwuwar mayar da Otal din Daula zuwa gidan zama.
Sanarwar ta ce kamfanoni biyu – LAMASH Properties Limited da FARI Properties Limited – sun gabatar da shawara ga majalisar zartarwa ta jihar Kano bisa tsarin “Build-Operate-Transfer”.
Da yake jawabi a madadin LAMASH Properties Ltd., Rabi’u Sa’id, ya ce kamfaninsa zai yi amfani da harabar “Gidan Sa’adu Zungur” ta Kamfanin jaridar Triumph don samar da “Kasuwar Canjin Kuɗaɗen Ƙasashen Waje”.d
Mista Sa’id, wanda Injiniya ne ya ce kamfaninsa zai samar da cikakken tsaro da sauran abubuwan more rayuwa kamar yadda ake samu a biranen da ake hada-hada kamar Legas ko Dubai.
Haka kuma, wakilin FARI Properties Ltd., Abdulkadir Abdulkadir, ya gabatar da shawarar samar da gida na alfarma mai cin iyali 57 da kayan more rayuwa a harabar Otal ɗin Daula.
“Yayinda gwamnati za ta samar da fili a matsayin kadara, kamfaninmu zai samar da kudade da kwararru don gudanar da aikin”, in ji Mista Abdulkadir.
Da yake maraba da wadannan shawarwari, gwamna Ganduje ya ce ya damu da yanayin tsaro a kasuwar canjin kudaden kasashen waje ta WAPA, wadda take kusa da Kamfanin Jaridar Triumph, wanda yake aiki a tsittsinke.
“Kamfanin jaridar Triumph yana buƙatar waje mai faɗi a muhalli mai nutsuwa da kayan aiki na zamani don mayar da shi kamfanin gwamnati da zai iya jurar wahala”, in ji gwamna Ganduje.
Idan dai ba a manta ba, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaɓen 2019 a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya maka gwamnatin Gwamna Ganduje a kotu bisa shirinta na cefanar da gine-ginen gwamnati.
A martaninsa, Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa tana mayar da gine-ginen gwamnati ne da aka yi watsi da su zuwa abubuwan amfani.
“Maimakon barin gine-gine masu amfani su lalace, muna duba shawarar yadda za mu mayar da su ayyuka da za su canza tsarin Kano su kuma riƙa samar da kudade ga jihar.
“Muna buƙatar mu zama masu hikima wajen tabbatar da mun mayar da waɗannan gine-gine abubuwa masu amfani da za su tabbatar da dorewar birnin Kano.
“Saboda haka ‘yan adawa ba za su hana mu cim ma burinmu ba”, in ji shi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Inganta Cloud Journey

Next Post

Taimakon Allah Ne Jigon Samun Zaman Lafiya A Masarautar Bauchi —-Sarkin Bauchi

RelatedPosts

Buba Marwa Ya Zama Sabon Shugaban Hukumar NDLEA

Buba Marwa Ya Zama Sabon Shugaban Hukumar NDLEA

by Abdullahi Muhammad Sheka
6 hours ago
0

Daga Abba Ibrahim Gwale, Shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince...

Kananan Hukumomin Jihar Kano

Yau Za A Yi Karon Batta A Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano

by Abdullahi Muhammad Sheka
15 hours ago
0

 Jam’iyyu 11 ne za su fafata PDP Kwankwasiyya ta ce,...

Sojoji

Tsofaffin Sojoji Sun Nemi Karin Kudin Fansho

by Abdullahi Muhammad Sheka
15 hours ago
0

Kungiyar tsofaffin sojoji ta kasa reshen jihar Anambra ta bukaci...

Next Post
Taimakon Allah Ne Jigon Samun Zaman Lafiya A Masarautar Bauchi —-Sarkin Bauchi

Taimakon Allah Ne Jigon Samun Zaman Lafiya A Masarautar Bauchi ----Sarkin Bauchi

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version