Connect with us

LABARAI

Ganduje Zai Samar Da Kayan Koyar Da Sana’o’i Na Naira Biliyan 2.5

Published

on

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin sayo kayan koyar da Sana’u irin na zamani daga Amurka domin horar da matasa a katafariyar cibiyar koyar da sana’u da Gwamnatin Kano ke aiki ginawa. Cibiyar koyar da sana’un da ake ginawa a garin Gurjiya dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu, kilomita kadan daga kwaryar birnin Kano.
Gwamna Ganduje ya bayyana cewa mun bayar da umarnin sayo kayan harkokin koyar da sana’u na sama da Naira Biliyon 2.5 kamar yadda itama cibiyar aka tsara zata lakume yawan wancan adadi na Naira Biliyon 2.5, yace muna son samar da wani abu da zai tabbatar da tallafawa matasa musamman tsare tsaren ayyukan wannan Gwamnati, kamar yadda darakta yada labaran Gwamna Ganduje Malam Abba Anwar ya bayyana.
Hakazalika Gwamna Ganduje ya bayyana cewa an samar da sana’u kala 24 domin horar da matasa a wannan cibiya, ya ci gaba da cewa Gwamnatin Kano tare da hadin guiwa da wasu kwararrun masu ruwa da tsaki wanda aka hada karfi domin samar da sana’u iri daban daban har guda 24.
Alokacin kaddamar sa harsashin ginin wannan cibiya da ka gudanar a farkon wannan shekara. Gwamna Ganduje ya sanar da mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo cewar Gwamnatin Kano ta rungumi wannan shiri domin daga darajar dubun dubar matasa tare da fitar dasu daga cikin kangin talauci. Yace Mai Girma Mataimakin shugaban Kasa muna yin duk mai yiwuwa domin kamanta irin kokarin da Gwamnatin tarayya ke yi na ganin matasa sun dogara da kansu.
Kwanan nan ma sai da Gwamnatin Kano cikin wani shiri na samar da kudade ga matasa inda aka rabawa mutane 8,800 naira dubu ashirin ashirin ga maza yayinda mata suka yi hafzi da Naira dubu goma sha biyar, Gwamna Ganduje yace Gwamnatin Knao na yin wannan ne domin tabbatar da ganin matasa sun zama masu dogaro da kai ta hanyar sana’u irin na zamani. Ana kyautata zaton Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da zuwa bude wannan katafariyar cibiya idan aka kammala aikinta, wannan na nuna irin damuwar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yiwa harkokin cigaban matasa a cewar Ganduje.
Idan aka kammala aikin cibiyar Gwamnatin Kano ce za ta dauki nauyin matasa ‘yan asalin Jihar Kano, ya yinda sauran matasa daga sauran Jihohin za su biya kudin horarwar. Ganduje yace yanzu haka mun tura wasu daga cikin jama’armu zuwa kasar Amurka domin samun horon yadda ake amfani da wadannan manyan na’urori da muka samar a wanna cibiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: