Daga Maje El-Hajeej Hotoro, Kano
‘Ga Kwankwaso Ga Ganduje Su Za Mu Bi Ba Karya Ba’
Wannan daya ne daga cikin fitattun wakokin siyasar tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanatan Kano ta Tsakiya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma tsohon mataimakinsa sannan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje. A tarihin siyasar jihar Kano ba a taba yin Gwamna da mataimakinsa da suka samu alaka kamar Kwankwaso da Gganduje ba. Kamar yadda a tarihin siyasar jihar ba a taba yin Gwamna da mataimakinsa da suka yi shekaru takwas a tare ba sai Kwankwaso da Ganduje. Wannan ya sa da Kwankwaso ya gina rukunin gidajen Kwankwasiyya City sai da ya gina BANDIRAWO City. A yayin da suke yakin neman zaben 2011 fitacciyar kalmar da Ganduje ya rika amfani da ita kenan ‘Bandirawo’ wacce kalma ce ta harshen Fillanci da ta ke nufin ‘Dan uwa’. A saukakakken harshe idan ka kira Kwankwaso da Ganduje DANJUMA da DANJUMMAI ko kuma HASSAN da HUSSEINI wannan suna ya dace da su babu tantama. Duk da dai Ganduje ya yi wa Kwankwaso tazara a shekaru.
A yayin da Kwankwaso ya zama Gwamna a jihar Kano shekarar 1999, tare da Ganduje suka yi duk abinda suka yi suka kuma tafi a tare yayin da Shekarau yayi nasarar lashe zaben 2003. A wata ruwayar Kanawa suna fadin cewa, da Kwankwaso ya zama Ministan tsaron Najeriya tare suka tafi da Ganduje suka yi suka gama. Kazalika da Kwankwaso ya zama wakilin Dafur tare suka kara rankayawa suka tafi da Ganduje. Bugu da kari da Kwankwaso ya dawo neman kujerar jihar Kano bayan shekaru takwas rabon sa da kujerar tare suka yi yakin neman zabe da Ganduje kuma dawo da Ganduje a matsayin Gwamna da mataimaki. Wannan ya sa suka kafa tarihi a siyasar jihar Kano da babu irin sa. Kwankwaso ya zama Gwamna da yayi shekara takwas ba ya kan kujera ya dawo ya karbi a bar sa. Ba a taba haka a jihar Kano ba da ma fadin Najeriya baki daya. Yayin da Ganduje ya zama mataimakin Gwamna da ya yi mulki har wa’adin mulki zango biyu. Shima ba a taba haka ba a jihar Kano.
A yayin da Kwankwaso ya kusa kammala wa’adin mulkinsa an shiga rudanin wa ye zai zama magajin sa, wasu rahotanni a jihar sun ruwaito Kwankwaso bai so ba wa Gganduje kujerar ba saboda yanayin yawan shekarun sa da kuma ba zai iya rike jihar kamar yadda ya bar masa ba. Lokacin guda gami da raya akidar Kwankwasiyya da kuma karasa muhimman ayyukan da ya bari. An tayar da jijiyoyin wuya an shiga an fita daga karshe Allah Ya tabbatar da Ganduje a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar APC. Duk da dai Ganduje na da matsalar rashin farin jinni a idon Kanawa bai samu matsalar talla ba sakamakon farin jinni Kwankwaso da kuma guguwar Buhari. An buga zabe kuma Ganduje ya kai ga nasara a matsayin gwamnan jihar Kano. Wanda Hakan ya sa ya kafa tarihin siyasar da babu irinsa a jihar Kano.
Na farko wani Gwamna bai taba kamo hannun wani ya zama Gwamna ba a jihar Kano sai Kwankwaso da ya kamo hannun Ganduje. Kamar yadda wani mataimakin Gwamna bai taba zama zababben gwamnan jihar ba sai akan Ganduje. Jim kadan bayan rantsuwa sai aka jiyo Ganduje na shelantawa Kanawa cewa. ‘Yadda Dillin Ta Kan Yi Dillin Haka Dillin Ta Kan Yi Dillin. Yadda Kaza Ta Kan Yi Kwan Nan Haka Ma Kwan Nan Ya Kan Yi Kaza’. Wanda aka fassara a matsayin sabon salon zaurancen siyasa da ke nufin yadda Kwankwaso ya yi haka shi ma Ganduje zai yi. Amma ba da jimawa ba sai aka fara jiyo kishin-kishin an samu matsala tsakanin Kwankwaso da Ganduje. Hakan ya bayyana karara yayin da mahaifiyar Ganduje ta rasu Kwankwaso ya zo gaisuwa aka samu cece-kuce tsakanin magoya bayan su.
Tukunyar siyasar jihar ta fara tafarfasa ta inda magoya bayan Ganduje suka zo suna sukar Kwankwaso akan tayar da hargitsi a yayin ziyarar ta’aziyyar babar Ganduje. Wannan ya sa suma magoya bayan Kwankwaso mayar da martani. Wasu da suka rasa dama suke kuma ganin ta hanyar jefa rikici a tsakanin aminan biyu ne kadai za su samu dama, sun yi amfani da wannan dama suka yi ta kara iza wutar rikicin. Kana kuma lokacin guda wasu daga cikin masu adawa da Kwankwaso suma suka kara sa hannu a rikicin har ya gagari sulhunta tsakanin su. Komai ya fito fili yayin da Ganduje ya bayyanawa duniya cewa, dama rikicin ya dade kawai yakana ya ke yi. A cewar sa bayan an rantsar da shi Kwankwaso zai tafi Abuja ya raka shi wajen motar sa, Kwankwaso yayi ta surfawa Ganduje zagi kamar wani karamin yaro. Kuma dama ya fada ya ce zai raba kafarsa daya a Abuja daya kuma Kano, idan bas u yi yadda ya ke so ba zai nannade kafar wanda ya dawo ya kifar da gwamnati.
Wannan rikici bai yi wa masu hankali da tunani dadi ba ta yadda suka nemi sulhunta tsakanin su, amma duk da haka ba a kai ga samun nasarar ba. Domin yanzu Gganduje zai furta maganar sulhu gobe sai a ji ya furta wata kalmar da ta ruguje waccan. Daga cikin fitacciyar maganar da yayi ita ce, an yi aiki an kuma yi aika-aika, da kuma shan alwashin zai fede biri har wutsiya. Duk da kiraye-kirayen da ‘yan adawar Kwankwaso suka rika yi akan ya bayyana aika-aikar, har zuwa rana irin ta yau Ganduje ya kasa bayyanawa. Kamar yadda da bakin sa ya fito ya jadaddawa masu son ya fede biri cewa WALLAHI BA ZAN FEDE BA.
A cewar wasu masu sharhin siyasar jihar sun ce rikicin ya samo asali ne yayin da Kwankwaso ya shaidawa Ganduje wasu masu tsananin adawa da shi da kada ya sake ya jawo su cikin mulkinsa. Kana kuma jagororin Kwankwasiyya da ya dasa a wasu muhimman mukamai kada ya taba su. Amma Kwankwaso na damka masa komai ya janyo su jikinsa. Kana kuma da rikici ya kazanta Ganduje ya rika bin manyan yaran Kwankwaso yana cire su daga cikin gwamnatin. Fitattu daga ciki sun hada da Rabi’u Sulaiman Bichi wanda a baya shine sakataren gwamnatin jiha, sai kuma Haruna Doguwa wanda shine shugaban jam’iyyaya maye gurbinsa da Abdullahi Abbas wanda aka yi shaidar ba ya kaunar Kwankwaso ko daidai da kinti daya. Sakamakon zargin ya hana mahaifinsa mukamin sarkin Kano ya nada Muhammadu Sanusi II.
Rikicin yayi naso zuwa majalisar dokokin jihar ta yadda duk mai son zama lafiya sai ya cire jar hula. Haka ya kar naso har zuwa ‘yan majalisar wakilai ta tarayya inda suka rika rige-rigen cire jar hula. Kafin a je ko ina sai ga shi an amince da kudirin goge sunan Kkwankwasiyya daga makarantun jihar da sauran muhimman gine-gine. Haka aka ware miliyoyin Nairori aka shiga aiki ba jib a gani, duk kuwa da irin bakar sukar lamarin da Kanawa suka rika yi. Bayan wannan gwamnatin jihar Kano ta sauya sunan wasu manyan gine-gine irinsu Kwankwasiyya City, Amana City da kuam Bandirawo zuwa sunan manyan malaman kungiyoyin addini na jihar. Sauya sunan katafariyar jami’ar North-west zuwa marigayi Maitama Sule shima ya bar baya da kura. Sai ga shi kwanan nan an sauya sunan makarantar Gobernors College zuwa Mairo Tijjani Girls Science & Technical College.
Aminan Kwankwaso a yayin da ya ke Gwamna sun rikide sun koma gawurtattun makiyan Kwankwaso a bayan Ganduje. Irin su Ali Baba A Gama Lafiya a baya har sbo ya rika yi akan kare manufofin siyasar Kwankwaso. Amma a halin yanzu Ganduje ya ja shi a jiki ya kuma mayar da soyayyar sa kan Ganduje ya mayar da kiyayyar kan Kwankwaso. Dan majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Bbirni Baffa Bbabba Dan Agundi na daga cikin wadanda Kwankwaso ya ba wa tikitin wannan kujera da ya ke kai. Amma a kwanan nan ya zama daya daga cikin jagororin afkawa jagororin Kwankwasiyya da hari a yayin bikin hawan Daushe. Wannan zargi ne daga bakin jagororin Kwankwasiyya kuma har rana irin ta yau ya kasa karyatawa. Dama tuni Abdullahi Abbas ya ayyana duk inda ake taro wani ya zo da jar dara a shafa masa jini a jiki. Wanda a baya shima an zarge shi da jagorantar yamutsi a yayin zaben cike gurbi na karamar hukumar Minjibir.
Furucin Ganduje akan Kwankwaso makiyin Buhari ne ya bayyana karara babu sulhu a tsakanin su. Kwankwasiyya sun yi sabuwar hular Kano ba sulhu yayin da ‘Yan Gandujiyya suka yi shege ka fasa. Kama mawaki Sadik Zazzabi sakamakon yi wa Kkwankwaso waka da hukumar tace fina-finan jihar ta yi, a bayyana ya nuna wutar gabar fa sai Allah. Babu jimawa kuma aka biya Rarara kudi yayi sabuwar waka yana cin zarafin Kwankwaso. Aka kuma kyale shi ba wani hukunci ko tuhuma. Zuwa yanzu dai ba a ji komai daga bakin Kwankwaso ba, face magoya bayan sa da suka himmatu da kiran Ganduje a matsayin Butulu. Yayin da mawakin Ganduje Ibrahim Ibrahim ya ce ‘Gandujiyya Halacci ce shi kuma kare mutunci wannan ba ya nufin Butulci’. Amma ko ma menene Ganduje ya dage ya ki cire jar hula wacce ‘yan Kwankwasiyya suke kallo a matsayin ta su ce.