Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Gangamin Wayar Da Kai A Kan Fyade Na Unguwar Rimi Kaduna Ya Kayatar

by
2 years ago
in RAHOTANNI
2 min read
Gangamin Wayar Da Kai A Kan Fyade Na Unguwar Rimi Kaduna Ya Kayatar
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Hukumar Alhazan Kogi Ta Fara Shirin Bita Ga Maniyyata

Fashewar Gas A Kano: Ministar Jinkai Ta Nemi A Dauki Matakan Riga-kafi

Fyade a cikin al’ummar mu ta zama wata annoba, ta yanda babu karami ko babba, mace ko namiji da ya tsira.
Dalilin haka ya sa daukacin al’ummar gundumar Gabasawa musamman Unguwar Rimi tare da hadin gwiwar kungiyan mata masu koyar da sana’oi (WOSI) suka shirya taron wayar wa al’umma kai da kuma gangami a kan maudu’i guda biyu: Na farko, Dalilan da suke jawo hauhawan fyade da kuma hanyoyin da za’a kare afkuwan su. Na biyu kuma Hakkin Iyaye domin bayar da kariya daga faruwan fyade a kan kananan yara.


Kwamitin tsare-tsare karkashin shugabancin Hon Nuhu Sani (cigarin UnguwarRimi) da mataimakiyan sa Hajiya Hafsat Sani (Assabur), sakataran tsare-tsare Mai-unguwa Alh Haruna Mu’azu, sakataran kudi Hon Sule Wada da sauran mambobin kwamititsare-tsare sun zagaya ta yanda suka samu hadin kan kungiyoyin sa Kai na unguwan sama da kungiya talatin (30). Haka zalika sun sama tattaunawa da babban jami’an lafiya ta asibitin unguwan Rimi ta yadda aka sama kididdiga na akalla akwai matsalar fyade sama da guda dari uku (300). Su ma jami’an tsaro wanda suka hada da jami’an ‘yan sanda karkashin DPO na unguwan Rimi, jami’an sa Kai na KADbS da cibilian JTF duk sun sanar wa da kwamitin tsare-tsare irin hauhawan matsalar fyade yanda ta ta’azzara.
An gudanar da taro ranar asabar 19 ga watan satumba, 2020 a cikin makarantan firamare ta unguwan kudu, unguwan Rimi kaduna.
An samu halartar manyan baki, wanda suka hada da Hajiya Maryam Mu’azu ( Darektar matasa ta ma’aikatan kula da jindadin al’umma da kyautata rayuwa) wacce ta wakilci kwamishiniyar ma’aikatar Hajiya Hafsat Muhammed Baba, Hakimin Gundumar Gabasawa, Dagatai, Babban Mai bawa gwamnan jihar Kaduna shawara kan kyautata rayuwan al’umma Hajiya Zainab Shehu, Alhaji Umar Ibrahim Dan-Adda wanda shi ya kasance uban taro, Barista Abdullahi Mukhtar Muhammed MON (tsohon shugaban Hukumar Aikin Hajji ta kasa), Hon Alhaji Sani Suleiman (tsohon shugaban karaman hukuman kaduna ta arewa) Wanda suka shugabanci taro, Suma sun sama wakilci, kasilan mazaban Gabasawa Hon Ibrahim Ahmed wanda ya kasance babban mai masaukin baki.
Taro ya gudana ta yanda kunkiyan sa Kai ta matasa (COGYST) ta gudanar da wasan kwaikwayo dan jawo hankalin al’ummahanyoyin da fyade kan afku da kuma matakin da ya kamata a dauka.
Manyan Baki masu fadakarwa sun hada da profesa Hauwa E. Yusuf ta jami’an jahar Kaduna wacce ta fadakar akan matsalar fyade da Hakkin dan-adam idan matsalar fyade ta afku. Barista Othman Aminu Bamalli ya fadakar akan hanyoyin shari’a da za’abi idan hakan ta faru. Sheikh Musa Tanimu yayi wa’azi akan tanaje-tanajan addinin musulunci. Reb. Dr. Zakariya Bulus Takore na chucin ECWA Goodness unguwan maigero kaduna Shima yayi wa’azi akan tanaje-tanajan addinin kirista. Alhaji Adamu Yusuf (shugaban kungiyan ‘yan Jarida ta kaduna) yayi jawabi akan irin gudunmawan da ‘yan Jarida suke badawa domin yaki da matsalar fyade. Hauwa Ahmed ( shugaban sashin binciken lafiya na asibitin unguwan Rimi) tayi jawabi akan kulawa da lafiya da kuma kididdigan hauhawan matsalar fyade a unguwan Rimi. DPO unguwan Rimi ya karfafawa al’ummacewa hukumansa baza suyi
Kasa a gwiwa ba wajan dakile faruwan fyade ba.
An gabatar da lambobin yabo ga wasu fitattun ‘yan unguwa wadanda suka bada gudunmawan su wajan cigaban unguwa.
Daga karsh an gabatar da gangami kuma an zagaye daukacin fadin unguwan domin nuna rashin yarda da afkuwan fyade a cikin wannan al’umma inda lamarin ya kayatar kwarai da gaske.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Mata Masu Kananan Sana’o’i Sun Kusa Bankwana Da Talauci A Kano – Fatima Dala

Next Post

An Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Sake Gina Babban Titin Gombe Zuwa Maiduguri

Labarai Masu Nasaba

Hukumar Alhazan Kogi Ta Fara Shirin Bita Ga Maniyyata

Hukumar Alhazan Kogi Ta Fara Shirin Bita Ga Maniyyata

by Ahmed Muhammad Dan'asabe
19 hours ago
0

...

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

Fashewar Gas A Kano: Ministar Jinkai Ta Nemi A Dauki Matakan Riga-kafi

by
20 hours ago
0

...

Baki Biyu Bai Dace Da Matsayin Amurka Ba

Baki Biyu Bai Dace Da Matsayin Amurka Ba

by CMG Hausa
23 hours ago
0

...

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

by
3 days ago
0

...

Next Post
An Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Sake Gina Babban Titin Gombe Zuwa Maiduguri

An Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Sake Gina Babban Titin Gombe Zuwa Maiduguri

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

 

Loading Comments...
 

    %d bloggers like this: