Connect with us

LABARAI

Gangamin Yajin Aikin Ma’akata Ya Yi Tasiri A Abuja

Published

on

Kungiyoyin kwadago sun samu nasarar dakatar da ayyuka a ma’aikatun gwamnatin tarayya da makarantu da ke babban birnin tarayya Abuja, inda aka wayi gari a wannan Alhamis yawancin manyan benaye da ke dauke da manyan ma’aikatu suka rufe ba tare da kowa ya fito aiki ba, lamarin da ke nuna cewa kungiyoyin ma’aikatan sun samu nasara kan fara wannan yajin aiki da nufin a tabbatar da alkawarin karin albashi da gwamnatin Nijeriya ta yi wa ma’aikatan don su samu sukunin gudanar da rayuwar su cikin walwala da jin dadi.

Wakilin mu ya kasance cikin wani gangamin kungiyar nakasassu daga sassa daban-daban na kasar nan inda suka zo birnin Abuja da nufin jan hankalin gwamnati don ta duba matsalar cin hanci da rashawa da ya yi katutu a Nijeriya.

Don haka, ya lura yawancin manyan ma’aikatun da suka hada da na kudi da na shari’a da ma’aikatar lafiya  da sauran su duk a rufe suke har da sakatariyar gwamnatin tarayya, lamarin da ke nuna yajin aikin ya samu karbuwa a babban birnin tarayya Abuja.

Saboda haka akwai bukatar wannan gwamnati ta shugaba Muhammad Buhari ta waiwayi alkawurran da ta yi wa ma’aikata na karin albashi a cikin watan Satumba amma alamu na nuna wannan lamari ba zai yiwu ba a daidai lokacin da shugabannin da ke mulkin kasar nan a wannan lokaci ke neman goyon bayan ma’aikata don a sake zabar su a matsayin shugabanni, duk

da cewa yawancin alkawurran da suka yi ba a cika su ba illa dan abin da ba za a rasa ba.

Don haka ya kamata wannan gwamnati ta shugaba Muhammadu Buhari ta dauki lamurran cika alkawari da muhimmanci musamman game da al’amarin da ya shafi ma’aikata da kuma daukar sabbin ma’aikata abu ne da ke bukatar a tabbatar da komai ya inganta saboda akwai tsananin wahala a kasar nan, wacce ma fi karancin albashi Naira dubu 15 a kananan hukumomi da jihohi yayin da kuma a gwamnatin tarayya ake karbar Naira dubu 18 wanda bai wuce kudin buhun shinkafa ba a wannan lokaci.

Kungiyoyin kwadagon sun samu nasara a wasu wurare yadda har minista ta je wata ma’aikata za ta shiga ‘yan kwadagon sun kore ta. Kuma ma’aikata sun yi na’am da wannan shirin yajin aiki saboda yadda suke shan wahala na tashin farashin kayayyaki da shiga kuncin rayuwa. A yayin wannan yajin aiki harkokin kasuwanci da gidajen mai  da kasuwanni sun fito suna gudanar da harkokin su kamar yadda aka saba musamman a babban birnin tarayya Abuja a wannan alhamis. Lamarin da ke nuna akwain bukatar gwamnati ta zauna da shugabannin kungiyoyin kwadagon don a samu mafita game da mawuyacin halin da ake ciki na kara kudi ga sauran kayan more rayuwa.

Don haka akwai bukatar a cire son rai da son zuciya a zauna a sasanta a fahimci hakurin da ma’aikatan kasar nan ke yi na hakuri da talauci yadda albashin Sanata daya na iya biyan bukatar  kananan ma’aikata dubu alhali kasuwa guda ake shiga, kuma shi shugaban kasa Buhari lokacin da yake yakin neman zabe ya yi kuka da hawayensa na cewa ma’aikata da talakawa na wahala, amma kuma hawan sa ke da wuya ya mance da cika irin wadannan alkawurra.
Advertisement

labarai