Ali Abubakar Sadik" />

Gangankon Azzalumai

Ranar 11 ga Oktoba, 2018 ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya sulhunta da babban abokin adawarsa na tsawon shekaru 15, wato tsohon mataimakinsa Atiku Abubakar, a katafaren dakin nazarinsa na biliyoyin Nairori a garin Abeokuta. Ba wanda ya yi mamakin ganin fuskoki irin na su Mathew Hassan Kukah, Ahmad Gumi, Oyedepo da sauran manyan kasar nan wadanda ke hankoron kawar da gwamnatin Buhari.

Azzalumai ko’ina cikin fadin kasar nan na kai-komo da hada karfi da karfe domin ganin sun kora Buhari zuwa Daura. Amma ina tabbatar mu su cewa za su sha mamaki na karshe a rayuwarsu, domin Baba sai ya kora su ritayar karfi-da-yaji daga harkokin siyasar kasar nan, inda bayan wa’adin mulkinsa na biyu a 2023 zai mika mulki ga sabbin jini.

A tarihin kasar nan ba a taba samun shugaban da ya sami dama irin wacce Obasanjo ya samu ba, domin dai daga kurkuku, inda ya ke gab da mutuwa sai Allah ya tsamo shi kuma ya zarce zuwa fadar mulkin Najeriya. Maimakon Obasanjo ya godewa Allah da irin wannan ni’ima da ya yi ma sa sannan ya saka wa ’yan Najeriya da su ka yi cincirindo wajen zabar sa a matsayin sabon shugaba, sai ya yi akasin haka. Mulkinsa ya bude sabon shafi na cin hanci da rashawa tare da neman murkushe dimukuradiyya domin ya tsige shugabannin majalisa da gwamnoni bila adadin ta hanyar barazana da amfani da kudi. Mulkin nasa ya dawo da mummunan bala’in kashe-kashe na kabilanci da addini wanda ya salwantar da dubban rayukan ’yan Najeriya.

Obasanjo ya yi iya yinsa wajen ganin ya zarce a karo na uku a mulki, yadda a ka rika ba wa ’yan majalisun tarayya da su ka goyi bayan yunkurin nasa Naira miliyan hamsin. Talakawa sun tashi tsaye wajen yaki tare  da murkushe wannan yunkuri. Duk wanda ya yi mu’amala ta kusa da Obasanjo, kamar yadda ’ya’yan cikinsa da matansa su ka tabbatar, ba shi da yafiya har sai dai in ya yi ramuwar gayya. A bayyane ya ke cewa lokacin da ya gaza samun tazarcensa, ya huce a kan ‘yan Najeriya wajen kakaba mu su Jonathan, kuma kowa ya san irin yadda ya wajiga duk wani dan Najeriya, saboda sakarcinsa na rashin iya mulki.

Sannan a can baya mun ga yadda a zaben 2003 irin kaskancin da Atiku ya sa Obasanjo na zargin tsugunawa a gabansa ya roke shi a gaban mutane domin neman ya ba shi goyon baya, ya sa Obasanjo ya kullaci Atiku. Ya na cin zabe ya ce da wa Allah ya hada shi ba da Atiku ba? Sai da ta kai aikinsa na mataimakin shugaban kasa ya gagare shi, kuma ya yi kutu-kutun hana PDP ba shi takarar shugaban kasa a 2007. A shekaru 15 da su ka gabata, duk inda Obasanjo ya tsuguna sai ya soki lamirin Atiku, yadda har cikin shahararren littafinsa da ya zazzagi mutane, wanda gwamnatin Jonathan ta hana shi kaddamarwa a Najeriya, ya yi ikirarin cewa Allah ba zai gafarce shi ba idan ya goyi bayan Atiku.

Shi kuma Mathew Hassan Kukah, shahararren malamin addinin Kirista, wanda idan ya na zance sai ya burge ka saboda iya magana, amma zuciyarsa kuntatacciya ce wadda iliminsa bai bar ta ta kalli abubuwa bisa adalci ba. Ya na daga cikin wadanda su ka assasa rigingimun kabilanci da addini a Arewa domin kullum maganarsa ta tunzura Kirista ce da caccakar ’yan Arewa da nuna kyama ga Musulmi da Musulunci. Annabi Isa ya koyawa Kiristoci cewa “Idan an mare ka a kuncin dama, ka juya na hagu a kara marinka” amma su Kukah ba su yarda da wannan koyarwa ba.

Mutum ne mai son mulki da abin duniya yadda duk gwamnati da za ta biya ma sa bukata ya na tare da ita; misali irin gwamnatin Jonathan. Bai taba goyon bayan Buhari ba a rayuwarsa, saboda sanin cewa ba zai iya samun kwandala ba a gurinsa. Amma a na tabbatar da Atiku a matsayi dan takara ya garzaya kai caffa gare shi, musamman ganin yadda a ke zargin ya yi facaka da biliyoyin Nairori a dare guda wajen saye takarar PDP.

Wannan alama ce ta cewa jira kawai su ke a koma ’yar gidan jiya. A matsayinsa na limamin Kirista da su ke girmamawa ya ci a ce an gan shi a gaba wajen sulhunta bambanci tsakanin Musulmi da Kirista, amma ka taba jin ya yi babatu a kan haka? Ka taba jin ya yi Allah  wadai a duk inda a ka kashe Musulmi? Daya daga cikin umarni mafi girma a Linjila shi ne “Ka so makwabcinka”  Sannan Annabi Isa ya barwa duniya wani ma’auni na tantance mutanen kirki inda ya ce “Duk bishiyar arziki, ka na iya gane ta daga yayanta”. Don haka duk wani mutumin arziki, ba tare da la’akari da addininsa ba, ka na iya gane shi daga ayyukansa. Mutanen kirki kamar yadda Allah ya fada ma na a Kur’ani su ne wadanda duk inda alheri ya ke su na umarni da shi kuma su na hani da kaucewa sharri.

Dr. Ahmad Gumi, a daya bangaren, sai in ce har gara ma Kukah da shi, domin kuwa shi Kukah ya na son nasa, amma kowa ya san yadda Gumi ke nuna matsananciyar kiyayya ga ’yan Shi’a fiye da kafirai. Amma saboda rashin sanin ya kamata, Gumi ya fito ya na fada wa duniya cewa ya shiga tsakani, don sasanta Musulmi da Kirista (Atiku da Obasanjo) tare da kafa hujja da wani hadisi daga Manzon Allah (SAW). Babu laifi yin sulhu da kowa ko da kuwa a yanayin yaki ne, amma kuma shi Gumi ya nuna munafincinsa wajen yin hujja da wannan hadisin. Domin idan har ya yarda da hadisin a cikin zuciyarsa, da sai ya dawo cikin gida ya sasanta Musulmi, wato ya sulhunta kansa da ‘yan Shi’a. Amman zan iya rantsuwa cewa wallahi ba zai yi wannan sulhu ba amma ga shi ya na sulhunta Musulmi da Kirista. Shin akwai munafinci a nan ko babu?

Albasa ba ta yi halin ruwa ba, domin mahaifin Dr. Ahmad din, wato Marigayi Mahmud Gumi mutum ne mai yakana da tawali’u da tsentseni. A shekarun 1980 Mahmud Gumi ya dawo daga Saudia inda ya karbo kyautar sarki Abdul-Aziz tare da zunzuruntun kudi Riyal 250,000, amma ya rabar da wannan tsabar kudi kafin ya shiga gidansa. Amma sai ga shi Ahmad Gumi na bawa barayi fatawar su debi kudin gwamnati ba haram ba ne, tun da ya na kewayawa su na sam mi shi ko?

Idan mu ka dawo kan mai gayyar kuwa, wato Atiku Abubakar, sai ka ji mutane na cewa ai ’yan APC ba su san mai cin rashawa da hanci ba ne sai da ya koma PDP. Sam ba haka ba ne, domin sama da shekaru 15 kowa ya san halin Atiku game da cin hancin. A kurkusan nan, shugabar NPA ta dakatar da kamfaninsa na Intel saboda kin shigar da miliyoyin Daloli cikin lalitar gwamnati, sai da ya ga haza sannan ya amince su ka fara biya. Wannan ba rashawa ba ne? Akwai cikakken rahota da gwamnatin Amurka ta wallafa ’yan shekarun baya a shafin Homeland Security, wanda ya tabbatar da cewa gwanatin Amurka na zargin Atiku da shigar da kudaden haram kimanin Dala miliyan 40 kasar ta Amurka.

A na rade-radin cewa Amurka ta hana shi shiga kasarta kuma wani ma’aikacin diflomasiya ya tabbatar da zargi cin hancin a kan Atiku amma kuma saboda dokar Amurka ta hana jami’anta magana game da izinin shiga kasarta ya ce ba zai iya bayani a kan hana shi izinin shiga ba. Tabbas ne an daure wani sanatan Amurka abokin harkar Atiku a Amurka. A lokacin zaben fitar da gwani a Fatakwal, kowa ya shaida yadda rashawarsa ta bayyana inda ya fi kowa iya siyen kuri’a da biliyoyin nairori a cikin dare guda.

Da alamu dai, kamar yadda Obasanjo ya fada cikin littafinsa, Atiku mutum ne mai bin ‘yan tsibbu don haka ina ganin ‘yan tsibbun na sa sun tabbatar masa da zai yi mulkin Nigeria ne, watakila shi ya sa ya kwallafa rai duk shekarar zabe sai ka ganshi cikin zawarawa. Zawarcin nasa ya samo asali a 1993 inda ya kwabsa da Abiola da Kingibe ya zama na uku. Abiola ya nemi mai gidan Atiku, wato Shehu Yar’Adua, da ya saka Atikun ya janye masa da don ya kada Kingibe da alkawarin zai ba shi mataimaki. Bayan anyi haka sai wasu isassu a siyasar Nigeria su ka hana Abiola cika wannan alkwari aka kuma ba Kingibe.

A shekarar 1999, watakila domin a saka wa ‘yan PDM, wato yaran Shehu Yar’Adua, da Obasanjo ya ci zabe sai ya bawa Atiku mataimaki. A cikin shekaru uku Atiku ya zama dan siyasa mafi karfin fada a ji, yadda gwamnoni da shugabannin siyasa su ka yi masa mubayi’a. Sai da ta kai tsohon na Ota sai da ya durkusu  gaban Atiku ya na magiyar ya bashi goyon baya ya zarce. Wannan kunyata Obasanjo da Atiku ya yi, ta zama kuskuren Atiku mafi girma a siyasance. Obasanjo na dawowa karo na biyu ya ce da wa Allah ya hada su ba da Atiku ba? Ya hana shi aikinsa na mataimakin shugaba kasa kuma ya yi kutu-kutun yadda PDP suka hana shi takara sai da ya gudu ya bar jam’iyyar.

A karshe mu sani cewa Allah ya taimaki ‘yan Nigeria domin su ne su ke zabe ba manyan azzalumai ba, domin da su ke yin zabe, a yau ma sai Atiku ya kada Buhari. A yanzu lokacinsu ne na yin babatu, barazana, kisisina, munafinci, zagon kasa, tunzuri, korafi da duk wata illa da za su iya yi. Amma su sani cewa komai fadin duhu, idan aka kawo fitila kwaya daya sai ka ga ta haskake ko’ina. Buhari shine wannan fitila mai yakar duhun zalunci. Kuma bahaushe ya ce “Idan rana ta fito, tafin hannu bay a iya rufe ta.”

Exit mobile version