Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Garban Kauye Farawa Ne Allurar Dinke Barakar Kumbotso – Muslihu Yusuf Ali

by Muhammad
January 25, 2021
in RAHOTANNI
2 min read
Garban
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

An bayyana zaben Sabon shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Alhaji Hassan Garban Kauye Farawa da akayi cikin makon da ya gabata da cewa shi ne zai kasance allurar dinke barakar data jima tana addabar cigaban Karamar Hukumar ta Kumbotso, jawabin haka ya fito daga bakin zababben kansilan mazabar Guringawa dake yankin Karamar Hukumar ta Kumbotso  Alhaji Muslihu Yusuf Ali alokacin da yake zantawa da manema lambarai a Kano ranar lahadin data gabata.

Muslihu Ali ya ce, karamar Hukumar Kumbotso ta samu shugaban da Insha Allah zai kawo gagarumin ci gaba kamar yadda wadanda suka  gabata kowa ya Yi bakin kokarinsa. Musamman zaben da aka yiwa matashi mai cikakken kaunar cigaban wannan yanki, wanda aka hakikance yana da ingantacciyar tarbiyya musamman girmama na gaba da kuma yakana da hangen nesa.

Ya ce, “mun hakikance cewar wannan zubin da aka samu a shugabancin Karamar Hukumar Kumbotso da cewa lallai laya tayi kyan rufi, kuma muna kyautata zaton kwalliya zata biya kudin sabulu. Yace kasancewar sabon shugaban matashi Mai cikakken tarihin adalci da girmama na gaba.”

Saboda Haka sai ya bukaci al’ummar Karamar Hukumar Kumbotso sun kara himmatuwa wajen bayar da dukkan hadin kan da ake fata daga bangarensu, sannan ya bukaci kara kaimi wajen yiwa shugabanni da Kasa baki daya addu’o’in dorewar zaman Lafiya, karuwar arziki da kwanciyar hankali a Karamar Hukuma, Jihar da Kasa baki daya.

 

An Cafke Biyu Bisa Zargin Satar Mutane Da Dillancin Makamai A Kaduna

Daga Rabiu Ali Indabawa

 

Jami’an rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane da kuma wani dillalin makamai a jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO), ASP Mohammed Jalige, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da yammacin jiya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ya bayyana cewa, “a ranar 24 ga Janairu 2021 da misalin karfe 11:00 na dare jami’an ‘yan sanda na Jihar Kaduna da ke aiki da Operation Yaki, yayin da suke sintiri a kan hanyar Gamagira da Soba, da ke Karamar Hukumar Soba, Kaduna sun kama wani babur kirar Boder da ba shi da rajista kuma suka kama mutane biyu da ake zargi Masu garkuwa da mutane da aka bayyana sunansu; Musa Sabiu mai shekara 40 da Umar Sule mai shekaru 30 dukkansu daga Kauyen Tampol na yankin Karamar Hukumar Kachia Kaduna.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Kwamishinan ’Yan Sandan Ebonyi Ya Kama Hadiman Gwamnan Jihar Biyu Da Shugaban Karamar Hukuma

Next Post

Gwamnan Gombe Ya Mika Ta’aziyyar Rasuwar SS Sule

RelatedPosts

Tuhumar Malam Abduljabbar Za A Yi, Ba Mukabala Da Shi Ba– Sheikh Khalil

by Sulaiman Ibrahim
11 hours ago
0

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja Shugaban Majalisar Malamai na Shiyyar...

ISWAP

Boko Haram Ta Yi Garkuwa Da Ma’aikatan Jinkai Bakwai A Dikwa

by Sulaiman Ibrahim
12 hours ago
0

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri A harin bayan nan da mayakan...

Makanike

Shari’ar Gonaki: Kotu Ta Aike Wa Rundunar Soja Da Ma’aikarar Shari’a Sammaci

by Sulaiman Ibrahim
12 hours ago
0

Daga Isa Abdullahi Gidan ‘Bakko, Zariya Kotun daukaka kara dake...

Next Post
Sule

Gwamnan Gombe Ya Mika Ta'aziyyar Rasuwar SS Sule

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version