Daga Sulaiman Bala Idris
A ranar Lahadin makon da ya gabata, tsohuwar ministar kuɗi kuma shugabar hukumar GAƁI, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, ta gargaɗi ga Hukumar Bada Tallafi ta Duniya (IMF) da wasu cibiyoyin duniya da su riƙa taka-tsantsan da ƙungiyoyi masu zaman kansu waɗanda ke iƙirarin faɗa da cin hanci da rashawa a faɗin tarayyar Nijeriya.
Ta bayyana cewa, da yawan waɗannan ƙungiyoyi masu iƙirarin yaƙi da cin hanci a Nijeriya, suna fake wa da guzuma ne domin su harbi karsana. Kuma karnukan farauta ne na mutanen da ke cikin gwamnati.
Okonjo-Iweala ta bayyana haka ne Birnin Washington DC, dake ƙasar Amurka a wurin taron shekara-shekara wanda Babban Bankin Duniya da Hukumar Bada Tallafi suke shirya wa, mai taken ‘Yaƙi da Cin hanci da rashawa’.
“Duk yadda za ku dage, babu wani abu da za ku iya taɓuka wa daga waje. Kuna buƙatar sanin haƙiƙanin cibiya ko ƙungiya da mutanen da ke cikinta, domin fahimtar waɗanda a shirye suke su yi wannan aikin tsakaninsu da Allah, sai a taimaka musu.
“Saboda ni na san tsiyar ƙasa ta Nijeriya. A maimakon ku haɗu da ƙungiyoyi masu zaman kansu, za ku faɗa tarkon ‘yan wankiya ne, ma’ana ƙungiyoyi masu zaman wasu ɗaiɗaikun al’umma.
“Sannan kuma dole ku sani cewa, waɗannan ‘yan wankiyan ba ƙaramin wayo suke da shi ba. Ga su da dabaru iri-iri. Ba wai kawai sakaka suke gabatar da lamurransu ba. Suna ƙirƙirar ƙungiyoyi ne saboda su zamar musu mafaka. Don su ci gaba da yi wa al’umma kan ta waye.
“Ana buƙatar takatsantsan da kula. Sai an natsu za a gane ƙungiyoyin ƙwarai. Sannan muna da ƙungiyoyin na gaske, masu yin yaƙi da cin hanci da rashawa tsakaninsu da Allah. Ya kamata ku san waɗanda ke shirya muku ƙarairayi da waɗanda ke faɗin gaskiya a lamurransu.” Inji ta