Kungiyar ‘yan kasuwan mai masu zaman kansu ta Nijeriya (IPMAN) ta shawarci ‘yan Nijeriya da su yi tsammanin karin farashin mai a kwanakin nan masu zuwa. Ta bayyana cewa, farashin mai lita daya zai iya kai wa naira 195. Ta bayyana lamarin da rashin alkifla daga bangaren gwamnatin tarayya da kamfanin mai ta kasa (NNPC) wajen bayar da tallafi da matsalolin bututun mai da kamfanin kasuwancin mai da kuma kulawa da fanni ne ya haddasa wannan matsala.
NNPC ta za ta kara farashin mai ba har sai ta gudanar da taro a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadugo a karshen wannan wata.
Sai dai kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya (TUC) ta ce, ba za ta ce uffan ba har sai an kara farashin man a hukumance.
A nasa martanin, jami’in yada labarai na NNPC, Dakta Kennie Obateru ya ce, “NNPC ba ya shirin kara farashin mai a wurarin sari cikin watan Fabrairun shekarar 2021.”
Da yake magana da Abuja jim kadan bayan fitowa daga taro, shugaban kamganin Kakanda Oil and Gas Nigeria Limited, Danasabe Kakanda ya zargi gwamnati da bai wa masu zaman kansu wuraren sarin mai sama da kungiyar ‘yan kasuwa masu zaman kansu. Ya bayyana cewa, a ko da yaushe kungiyar ‘yan kasuwa masu zaman kansu ana barin su a baya wajen rarraba mai a cikin kasar nan.
“Bisa gazawar gwamnati, ‘yan Nijeriya su yi tsammanin sayan farashin mai kan naira 190 zuwa 190 ga kowacce lita.”
Shi ma shugaban kamfanin Foste Nigeria Limited, Cif Austin Erhabor ya bukaci ministan albarkatun mai, Cif Timipre Sylba ya yi amfani da kamfanin NNPC wajen bayyana wa ‘yan Nijeriya a kan an gyara fannin mai ko koma ba a gyara ba yana nan yadda yake.
“Lokaci ya yin a rarraba tsare-tsare daga cikin tattalin arziki. Kasuwancinmu ya bushe. Ta ya ya za a yi maganan gyara fannin mai sannan kuna bayyana farashin mai a hukumance.
Erhabor ya nuna damuwarsa na yadda ‘yan kasuwa suke fama da matsaloli wajen rarraba man a cikin kasar nan. Ya ce, bangaran yana fuskantar rashin dai-daituwa sakamakon manufofin gwamnati.
“Wannan wurare masu zaman kansu bai kamata su mallaki gidajen mai ba. Ya kamata kamfanin NNPC ya kasance shi ne dillali da kuma kungiyar ‘yan kasuwa,” inji shi.
Tsahon sakataren IPMAN, Dakta Emma Ihedigbo ya bayyana cewa, ‘yan kasuwan mai ba sa jin dadin yadda manufofin gwamnatin ke shafar bangaren kasuwancin mai.