Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

Gargadin Tsageran Neja Delta Ga IPOB; Ku Daina Danganta Mu Da Ku, Mu Ba ‘Yan Biyafara Bane

by Tayo Adelaja
September 19, 2017
in MANYAN LABARAI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja

Wata gamayyar tsageran yankin Neja Delta a ranar Lahadi 17 ga watan Satumbar 2017, sun bayyana cewa zasu kalubalanci duk wani yunkuri na son alakantasu da ‘yan kungiyar IPOB, ko kuma lissafa yankinsu a matsayin daya cikin biyafara.

samndaads

Tsageran sun fadi haka ne a wata takardar manema labarai da suka sake. Takardar ta samu sa hannun Janar John Duku, Janar Ekpo Ekpo, Janar Osarolor Nedam, Manjo Janar Henry Okon Etete, Manjo Janar Asukwo Henshaw da sauran mashahuran tsagera da ake takama da su a yankin na Neja Delta.

A takardar, tsageran na Neja Delta sun gargadi shugaban ‘yan kungiyar ta IPOB, da dukkanin sauran membobinta akan su kiyayi duk wani abu da ya shafi yankinsu na Neja Delta, musamman ma yankunan Jihar Ribas.

Haka kuma ‘yan tsageran sun mayar da raddi ga tsohon shugaban Kasa Obasanjo, a shawarar da ya bayar ta cewa a yi zaman sulhu da ‘yan biyafaran. Inda suka zarge shi da cewa shi a zamaninsa bai yi sulhu dasu ba, sai da ma yakarsu da yayi, ciki kuwa har da kulle Dokobu Asari da yayi.

Takardar ta ce; “Muna kira ga gwamnatin Nijeriya da ta bar ‘yan biyafara su balle, tunda sun ce sun gaji da zama a cikin Nijeriya. Ko ba komai ba mu fatan a afka cikin wani sabon yakin basasan.  Saboda irin wannan yunkurin na ‘yan biyafara ne ya janyo yakin basasan da aka gwabza a shekarun baya. Su kuma ‘yan biyafara, muna gargadinsu da su daina danganta mu da su, saboda mu ba ‘yan biyafara bane.” In ji tsageran.

 

 

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Dole A Zakulo Wadanda Suka Aukawa Hausawa A Kudu –Sarkin Kano

Next Post

ASUU Ta Janye Yajin Aiki

RelatedPosts

Beli

Ka Sake Ba Ni Beli – Maina Ga Alkali

by Muhammad
11 hours ago
0

Ya Ce, Da Gaske Ba Shi Da Lafiya Daga Khalid...

Bude Makarantu

Korona: Ba Ja Baya Ga Bude Makarantu – Gwamnatin Bauchi

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta...

Harshen Hausa

Taron ‘Waiwaye Adon Tafiya’: Masana Sun Damu Bisa Nakasta Harshen Hausa

by Muhammad
1 week ago
0

Akwai Damuwa Kan Yadda Zamani Ke Tafiya Da Al’adun Bahaushe...

Next Post

ASUU Ta Janye Yajin Aiki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version