Connect with us

LABARAI

Garkuwa: Boko Haram Ta Kashe Ma’aikatan Agaji A Borno

Published

on

Wasu mayakan da ake kyautata zaton na Boko Haram ne, sun kashe wasu ma’aikatan kungiyoyin bayar da agaji gaggawa biyar din da su ka yi garkuwa da su kwanan baya a jihar Borno.

Mayakan sun nuna yadda su ke fille kan ma’aikatan a wani faifan bidiyon da su ka fitar a kafofin sada zumunta na zamani, a yau (jiya) Laraba.

Mayakan da su ka gudanar da kisan, sun shaidar da cewa sun halaka ma’aikatan bayar da agajin gaggawar, wadanda ke aiki da kungiyoyin agaji daban-daban.

Faifan bidiyon mai dakikoki 35, wanda a ciki aka nuna wasu mutane rufe da fuskoki, tsaye a bayan wadannan mutane biyar da aka yi awon gaba da su; sun dunkusa a gabansu.

Yayin da kuma wata murya da harshen Hausa ana bayyana cewa,  “Wannan sako ne zuwa ga wadanda su ke amfani daku wajen sauya wa al’ummar mu imanin su (Addini).”

“A yau za ku gane cewa wadanda su ka dauke ku wannan aikin su na amfani da ku ne domin cimma muradin su, kuma ba su damu daku ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa mu ka sace ku, kuma gashi ba su damu da ku ba.

“Saboda haka mu na baku shawara ku tuba ku koma ga hanyar Allah, idan kuma ba haka ba, za mu rinka yi mu ku kwanton-bauna mu ci gaba da sace ku duk hanyar da ku ka biyo.

“Kuma idan ba su saurari gargadin da mu ke yi muku ba, za ku gamu da abinda wadannan ma’aikatan bayar da agajin gaggawa guda biyar su ka gamu da shi.”

Wanda mai wannan murya ya na kammala gargadin shi, shi ne sai daya daga cikin mayakan ya bayar da umurnin a dirka wa kamammun ma’aikatan bayar da agajin dalma, wanda kuma nan take, ya harbe mutanen wadanda aka daure fuskokin su da kyalle.

Bugu da kari, duk kokarin wakilin mu a jihar wajen jin ta bakin hukumomi dangane da lamarin ya ci tura.
Advertisement

labarai