Garkuwa Da Dalibai: Iyaye Sun Yi Zanga-zanga A Majalisar Tarayya

Majalisar Wakilai

Daga Sulaiman Ibrahim

Iyaye da membobin kungiyar Tarayyar Dalibai a ranar Talata sun yi tattaki zuwa Majalisar Dokoki ta kasa don neman a saki daliban Greenfield da aka sace.

Mutuna cewa an sace kimanin dalibai 22 daga harabar jami’ar a ranar 20 ga Afrilu.
Kungiyar karkashin jagorancin mai fafutukar hakkin Dan Adam, Deji Adeyanju ta taru a Unity fountain a cikin jerin gwano sannan suka nufi ginin Majalisar Dokoki ta kasa, suna neman a ceto rayukan daliban.
A cikin bidiyon da Adeyanju ya saka , iyaye da shugabannin kungiyar daliban sun rike alluna dauke da rubutu “Ku dawo da daliban mu”
“Ina kira ga gwamnati da ta ceto rayukan daliban, kar ta bari a kashe su a yau.”
Wannan na zuwa ne bayan masu garkuwan, sun lashi takobin kashe sauran daliban 17 idan ba a biya kudin fansa ba.

Shugaban masu garkuwan wanda ya bayyana kansa da suna Sani Idris Jalingo, yayin da yake magana a wata hira da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) ya ce za a kashe sauran daliban a yau Talata idan gwamnati ta kasa biyan bukatunsu.

A cewarsa, bukatar tasu ta hada da Naira miliyan 100 da babura kirar Honda 10.
A halin yanzu, an kashe biyar daga cikin daliban da aka sace a cikin mako guda yayin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya sha alwashin ba zai tattauna da ‘yan bindiga ba.

Exit mobile version