Abba Ibrahim Wada" />

Gasar CARABAO: An Hada Chelsea Da Manchester United, Ita Kuma Liverpool Da Arsenal

Matashin dan wasa, Reece James ya taka rawar gani a wasan da Chelsea ta sharara wa Grimsby Town kwallaye 7-1 a gasar cin kofin Caraboa Cup da suka fafata ranar Laraba bayan da James din ya ci kwallo ya kuma taimaka aka zura biyu a raga a wasan da Chelsea ta fitar da Grimsby mai buga gasar League Two ta Ingila daga gasar Caraboa ta bana.

Dan wasan mai shekara 19, shi ne ya bai wa Michy Batsuayi kwallon da ya zura a raga da kuma wadda ya buga wa Kurt Zuma ya ci cikin sauki kuma James shi ne ya ci wa Chelsea awallo ta biyar a wasan, sai kuma Batsuayi ya kara ta biyu da ya ci a fafatawar da aka yi a filin wasa na Stamford Bridge dake birnin Landan.
Chelsea ta kuma ci kwallo ta hanmnun Ross Barkley da Callum Hudson-Odai, yayin da Grimsby ta zare daya ta hannun Matt Green, kuma kwallo mai kayatarwa ya ci sai dai bayan an raba jadawalin zagaye na hudu Chelsea za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan zagaye na hudun a gasar ta Carboa Cup.
kungiyar ta ta kai wannan matakin ne, bayan da ta doke Grimsby Town 7-1, ita kuwa United a bugun fenareti ta fitar da Rochdale, bayan da suka tashi 1-1 haka kuma a kwai wani babban wasan da Arsenal za ta ziyarci filin wasa na Anfield domin fafatawa da Liverpool a karawar kungiyoyi 16 da suka rage a wasannin Caraboa na bana.
Haka kuma kungiyoyin da ke buga gasar League Two a Ingila Crawley da Colchester za su kece-raini a tsakaninsu sai kuma Southampton wadda ta fitar da Portsmouth kuma karon farko da ta ci kungiyar tun bayan shekara 35 za ta ziyarci Manchester City a filin wasa na Ettihad.
Haka kuma a kwai fafatawa tsakanin kungiyoyin da ke buga firimiya, inda Eberton za ta fuskanci Watford da gumurzu tsakanin Aston billa da Wolbes sai Leicester City za ta ziyarci Burton, yayin da kungiyoyin da ke buga League One a Ingila Odford za ta karbi bakuncin Sunderland.
Wasannin zagaye na hudu a Caraboa Cup:
Eberton da Watford
Aston billa da Wolberhampton Wanderers
Manchester City da Southampton
Burton da Leicester
Crawley da Colchester
Chelsea da Manchester United
Oxford da Sunderland
Liverpool da Arsenal

Exit mobile version