Gasar Cin Kofin Duniya: Katar Na Kashe Dala Miliyan 500 Duk Mako

Shugaban shirye-shiryen da kasar Katar ke yi domin karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta Duniya a shekara ta 2022, Hassan Al-Thawadi, ya musanta cewa takkadama tsakaninsu da wasu kasashen Larabawa ya tsayar da shirye-shiryen da ta ke yi, biyo bayan rufe iyakokin da Saudiya ta yi da kasar ta Katar.

A cewar Hassan, tasirin da wannan koma bayan Diflomasiyyar bai taka kara ya karya ba, kan shrin da suke na karbar bakuncin na gasar kwallon kafar ta duniya

Katar dai na kashe jimillar kudi dala miliyan 500 a duk mako guda, kan shirin da ta ke na karabar bakuncin gasar.

A ranar biyar ga watan Yunin da ya gabata ne kasashen Saudiya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da kuma Masar suka yanke hulda da Katar, bisa zarginta da goyon bayan ayyukan ta’addanci, ta hanyar tallafawa kungiyoyin da aka bayyana su a matsayin na ta’adda.

Exit mobile version