Real Madrid ta buga gasar cin kofin Copa del Rey a ranar Laraba, inda ta ziyarci kungiyar Alcoyano a wasan kungiyoyi 32 da suka rage a fafatawar kuma wannan ne karo na hudu da mai koyarwa Zinedine Zidane ya ja ragamar Real Madrid a Copa del Rey da bai taba lashe shi ba.
Kocin dan kasar Faransa ya lashe kofuna a Real Madrid, ciki har da gasar cin kofin zakarun turai na Champions League guda uku da La Liga biyu da European Super Cup biyu da Spanish Super Cup da Fifa Club World Cup, amma ban da Copa del Rey.
A kaka uku baya da ya ja ragamar Real Madrid, Zidane bai taba haura karawar daf da ta kusa da ta karshe ba wato quarter finals sai gashi a wannan kakar ma tun a zagayen kungiyoyi 32 anyi waje da kungiyar.
A shekarar 2017 Real Madrid ta yi kokarin lashe kofi uku har da biyu a Sifaniya da ya hada da na La Liga da Copa del Rey da kuma Champions League sai dai duk da haka Zidane bai samu nasara ba a gasar Copa Del Rey.
Kaka ta biyu da Zidane ya ja ragamar Real Madrid an kara yin waje da kungiyar a Kuarter finals a hannun Leganes sannan karo na uku kuwa shi ne wanda Real Sociedad ta yi waje da Real Madrid a Santiago Bernabeu daga Copa del Rey a wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.
Real Madrid wadda aka karbe Spanish Super Cup a hannunta a bana tana ta biyu a teburin La Liga tana kuma buga gasar Champions League a bana za kai zagaye na biyu amma a jiya kungiyar Alcoyano, wadda take buga gasa mai daraja ta uku a kasar Sipanya ta doke ta daci 2-1.