Gasar Firimiya Abar Tsoro Ce –Tuchel

Tuchel

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thomas Tuchel, ya bayyana cewa gasar firimiyar kasar Ingila bata da tabbas kuma abar tsoro ce saboda haka yana fatan kungiyarsa za ta farfado daga rashin nasarar da ta yi a wasan ranar Asabar.

A karon farko an doke mai koyarwa Thomas Tuchel a matsayinsa na kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea bayan kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion ta yi raga-raga da kungiyar da ci 5-2 a filin wasa na Stamford Bridge dake birnin London.

Chelsea ta kare wasan ne da ‘yan wasa 10 bayan an bai wa dan wasanta na baya, Thiago Silba jan kati sakamakon kama shi da aka yi da laifi har sau biyu kuma ana bashi katin gargadi.

Tuchel ya buga wasanni 14 ba a doke shi ba a dukkanin wasannin da ya buga a kungiyar, bayan Chelsea ta kori tsohon kociyanta, Frank Lampard a watan Janairun wannan shekarar da muke ciki.

Dan wasan Chelsea Christian Pulisic ne ya fara zira kwallo a raga, kafin a bai wa Thiago jan kati sannan ana dab da zuwa hutun rabin lokaci dan wasan West Brom Albion Matheus Pereira ya ci kwallaye biyu, ya zama ana nasara akan Chelsea da ci 1-2.

Mbaye Diagne ya ci wa West Brom kwallo ta uku yayin da kuma Callum Robinson ya rufe da sauran kwallayen a ragar Chelsea wanda hakan ya sa kociyan kungiyar, Sam Allardyce ya bayyana cewa wasan ya bashi mamaki.

Sakamakon wasan wani kalubale ne ga fafutukar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea take na kare gasar a cikin jerin kungiyoyin hudun farko domin samun gurbin zuwa gasar cin kofin zakarun Turai na kakar wasa mai zuwa.

Wannan ne karon farko da aka ci Chelsea kwallaye biyar tun shekarar 2011 da Arsenal ta zazzaga mata kwallayen kuma Thiago Silba mai shekara 36 a duniya shi ne dan wasa mafi tsufa da aka bai wa jan kati a kungiyar tun John Terry a shekarar 2016.

Exit mobile version