Daga Sulaiman Ibrahim,
Manchester City za ta karbi bakuncin Chelsea a filin wasa na Etihad a wasannin Firimiya na karshen makon nan.
City ta ci Arsenal a wasansu na karshe na gasar Firimiya inda ta kara tazarar maki goma a saman teburi.
A daya bangaren kuma, Chelsea ta buga kunnan doki ne da Liverpool 2-2 a karawar da suka yi a Stamford Bridge a gasar Firimiyar da ta gabata.
Man City za ta tayi rashin dan wasa Riyad Mahrez da ke wakiltar Algeria a gasar cin kofin Afrika da ake yi a Kamaru, yayin da Chelsea itama tayi rashin Edouard Mendy wanda shi ma yana wakiltar Senegal a gasar cin kofin.
Sauran Wasannin da za a buga a yau Asabar sun hada da:
Norwich City vs Everton
Wolves vs Southampton
Newcastle vs Watford
Aston Villa vs Man United