Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) ta kaddamar da gasar Lig ta kwallon yashi ta kasa, wato Nigeria ‘Beach Soccer League’ a turance, bayan an kwashe shekara da shekaru ana kiran hukumar ta kaddamar da gasar.
Shugaban hukumar ta NFF Amaju Pinnick ne ya jagoranci kaddamar da soma sabuwar gasar kwallon yashin ta Nijeriyar a ranar Lahadi inda kuma ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa gasar har ta zama babbar gasar da za a dinga bugawa.
Sabuwar gasar za ta rika gudana ne a karkashin hadin gwiwar hukumar kwallon ta kasa, da hukumar kwallon yashi ta duniya da kuma hukumar kula da kwallon yashi ta Afrika.
A wasan farko, kwallon yashin da aka fafata na rukunin farko, kungiyar Kebbi BSC ta lallasa Badagary United da kwallaye 4-2 kuma a ranar Asabar mai zuwa za a ci gaba da fafata wasannin kamar yadda aka tsara.
A sauran wasannin da aka fafata Anambra BSC ta lallasa Kwara BSC da kwallaye 5-2 ya yin da a rukuni na biyu, Igbogboa BSC ta doke takwarar ta Edo da 6-3, sai kuma Kada BSC da ta samu nasara kan Smart City da ci 6-4.