Kusan zamu iya cewa gasar laliga ta kasar Spaniya kungiyoyi biyu ne suka mamaye gasar, wato Real Madrid da Barcelona, sai dai akwai kungiyar Atletico Madrid wadda itama a yan shekarun nan ta taka rawar gani sosai.
Barcelona ta lashe gasar sau 24 a tarihi wanda hakan yake nuna cewa tana daya daga cikin kungiyoyin da suke haskaka gasar duba da irin yan wasan da kungiyar take dasu.
Hakan yana nufin idan aka raba kasar gida biyu to Barcelona zata dena buga gasar laliga kamar yadda fira ministan kasar ta Spaniya ya tabbatar inda yace idan har birnin na Catalunya ya balle daga hadaddiyar kasar Spaniya to kungiyar Barcelona bazata sake buga gasar laliga ba domin kundin tsarin kasar ta Spaniya bai bar wata kungiya tazo ta buga gasar kasar ba indai ba a kasar take a zaune ba.
Zai kasance kenan babu wata kungiya sai Real Madrid a kasar indai Barcelona tabar buga gasar, sai dai kungiyoyi irinsu Atletico Madrid da Sebilla da Balencia da Athletico Bilbao sune zasu kasance suna fafatawa da real Madrid wajen neman gasar laliga.
Real Madrid kenan zata mamaye gasar duk da daman har yanzu tafi kowacce kungiya yawan lashe gasar, sai dai ragowar kungiyoyin zasu fara kasha kudi domin gigawa da real Madrid din?