Gasar Sarauniyar Kyau: Cece-kuce Ya Barke Kan Shatu Garko

Sarauniyar

Daga Bello Hamza, Abuja da Abdullahi Moh’d Sheka,

Hukumar Hisbah a Jihar Kano na shirin gayyatar iyayen Shatu Garko wadda ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Nijeriya karo na 44 da aka yi ranar Juma’ar da ta gabata.

Shatu Garko, ‘yar shekara 18 daga Jihar Kano ta shiga gasar ce sanye da Hijabi a taron da aka yi a gaban dinbin jama’a a garin Legas.

Shugaban Hukumar a Hisbah, Sheikh Harun Muhammad Sani Ibn Sina, ya bayyana wa manema labarai cewa, shigar Shatu Garko gasar sarauniyar kyau abu ne da ya saba wa koyarwa addinin Musulunci, kuma ba za a amince da shi ba.

Ya kawo hujojji daga Alku’ani mai tsarki da hadisai, ya kuma kara da cewa, “Bincikenmu ya tabbatar da cewa, Shatu Garko ‘yar asalin Jihar Kano ce daga karamar hukumar Garko.

“A addinance, abu ne da aka haramta, bai kuma kamata mace ta bayyana al’auranta ba sai tafin hannunta da fuskanta suma sai ga muharramanta kwai, wato miji, ‘ya’ya da sauran ‘yanuwanta, abin har ya kai da yaranmu na shiga gasar bayyana tsiracci da suna sarauniyar kyau, tabbas wannan abu ne da ba za a amince da shi ba.”

Ya kuma ce, Hukumar Hisbah  na shirin gayyatar iyayen Shatu akan abin da ‘yarsu ta aikata.

Shatu Garko wata matashiya ce ‘yar asalin Jihar Kano da aka shelanta lashe Gasar Sarauniyar kyau ta kasarnan da aka gudanar cikin makon da ya gabata.

Shatu Garko, mai shekara 18, ta doke zaratan mata 18 a bikin da aka gudanar ranar Juma’a da dare a Landmark Centre da ke birnin Legas. Shatu ce mace ta farko mai hijabi da ta lashe gasar a tarihi kuma

wannan ne karo na 44 na gasar wadda ake kira Miss Nigeria a Turance. Nicole Ikot ce ta zo ta biyu, sai kuma Kasarachi Okoro da ta zo ta uku.

Ta karbe kambin ne daga hannun Etsanyi Tukura ‘yar Jihar Taraba, wadda ta lashe gasar a karo na 43 a Shekara ta 2019.

A cewar masu shirya gasar, wadda ta yi nasara za ta samu kyautar kudi Naira miliyon 10, da zama a gidan alfarma na shekara daya, da sabuwar mota, da kuma zama jakadiya ta musamman ga wasu kamfanoni.

Masu kula da gasar sun ce ana samun sabbin al’amura a kowace shekara game da matan da ke fafatawa tsawon shekara 44 da ake gudanar da ita.

A martaninta, Wakilyar Hukumar Kare Hakkin Dan’dam da Ilimantarwa (CHRICED), Zuwaira Umar, ta ce, wannan mataki na Hisbah ya sabawa hakkin Aisha Garko.

“Tana da damar da tsarin mulki ya bai wa dukkan ‘yan Nijeriya na ‘yancin mu’amala da kuma bayyana ra’ayi ba tare da takurawa ba. Babu wata doka a Kano da ta haramta abin da ta yi, in kuma ana maganar rashin tarbiya ne, abin da ta yi bai kai na yadda wasu yaran masu hannu da shuni suke yi ba shigar marasa mutunci a Kano.

“’Yar wani mai hannu da shuni a Kano ta yi shigar da ta fi na yadda Aisha Garko ta yi, wadda ma yi shigar mutunci a gasar da ta shiga ta kuma samu nasara. Na biyu kuma bata yi wannan abin da suke zargi ba a nan Kano, ba ma a Kano take zaune ba, a wajen Kano take zaune.”

Ta kuma kara da cewa, ba kyau ne kawai sharuddan zaban sarauniyar kyau ba a Nijetiya, cikin sharuddan a kwai ilimi da fikira da kuma irin gudummawar da mace ta bayar a bunkasa kasa da sauran su.

A nasa gudumawar, Tsohn Sanata daga JIhar Kaduna, Shehu Sani, ya yi tsokaci a kafar sadarwa ta Tweeter, inda yake cewa, “Shatu Garko ta shiga gasar ne a cikin shiga ta kamala. Bata sabawa wata dokar al’ada da ake dashi ba a yankin arewa. Akwai yaran masu hannu da shuni a arewacin kasar nan da suke shigar da ta fi haka muni ba tare da an hukunta su ba. Ina kira ga Hukumar Hisbah da su janye wannan barazanar da suke yi mata.”

A nata martanin, wata mai fafutukar kare hakkin al’umma, Aisha Yesufu, ta bayyana cewa, “Yanzu shike nan don ‘yata ta shiga gasar sarauniyar kyau sai Hisbah ta tuhume ni?! Wannan abin dariya ne! in har suka tare ni da wannan a ranar za su san cewa, dukkanmu mahaukata ne! aikin banza!”

Wani marubuci, Gimba Kakanda, ya jinjina lamari ne ya kuma bayyana ra’ayinsa a Twitter, inda yake cewa, gayyayar da aka yi wa Shatu Garko ba shi da wani muhimmanci.

Ya kuma kara da cewa, “A tunani na Hisbah na jin dadin wasa da hankalin Musulmai musammnan ‘yan Arewa. Gayyatar iyayen Shatu Garko ba shi da wani muhimmanci ko da kuwa menene niyyar yin hakan. Akwai manyan matsalolin da al’umma Musulmai ke fuskanta a kasar nan wanda shiga gasar sarauniyar kyau bashi a cikinsu a halin yanzu.”

Exit mobile version