A wasan karshe da aka fafata a yammacin jiya Lahadi tawagar kwallon kafa ta kasar Ghana ta lashe kofin gasar kwallon kafa ta kasashen yammacin Afrika WAFU, bayan ta samu nasarar lallasa Super Eagles ta Najeriya da kwallaye 4-1.
Bayan nasarar lashe kofin, tawagar kwallon kafar kasar ta Ghana ta samu kyautar Dala Dubu 100.