Connect with us

WASANNI

Gasar Zakarun Turai Ta Wannan Kakar Za Ta Fi Zafi – Shugaban UEFA

Published

on

Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai Alexandra Ceferin ya bayyana cewa gasar zakarun turai ta wannan shekarar zatafi ta kowacce shekara saboda yadda manyan kungiyoyi suka dawo gasar.

Shugaban ya bayyana hakane a wata hira da yayi da manema labara jim kadan bayan daya jagoranci raba jadawalin yadda za’a buga gasar a wannan kakar a babban dakin taro dake birnin Monaco dake kasar Faransa.

Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta fitar da jadawalin kungiyoyi 32 da za su fafata a gasar lashe kofin zakarun Turai, inda ta rarraba su zuwa rukuni 8 kamar yadda hukumar ta saba duk shekara

Rukunin farko na jadawalin, wato rukunin A ya kunshi kungiyoyi irinsu Atletico Madrid da Dortmund da Monaco da Club Brugge.

Sai kuma rukunin B da ya kunshi Barcelona daga Sipaniya da Tottenham ta Ingila da PSV ta kasar Holland sai kuma Inter Milan wadda tafito daga kasar Italiya

Akwai kuma rukunin C da ya kunshi PSG ta Faransa da Napoli ta Italiya da Liverpool ta Ingila da kuma Red Star Belgrade ta kasar Bulgeria

Yayinda rukunin D ya kunshi kungiyoyi irinsu Lokomotib Moscow ta kasar Rasha da FC Porto TA Portugal da Schalke da Jamus da kuma Galatasararay daga Turkiyya.

Akwai kuma rukunin E daya kunshi Bayern Munich daga Jamus da Benfica daga Portugal da Ajax daga Holland da kuma AEK Athens ta kasar Greece.

Ka zalika rukunin F ya kunshi kungiyoyi irinsu Manchester City ta kasar Ingila da Shakhtar ta kasar Ukraine da Lyon ta Farabsa da kuma Hoffenheim ta kasar Jamus

Rukunin G kuma akwai mai rike da kambu wato Real Madrid da Roma da CSKA Moscow ta Rasha da Viktoria Plzen daga Bulgeria.

Yayinda rukunin H kuma ya kunshi Juvntus ta Italiya da Manchester United ta Ingila da Valencia daga Sipaniya da kuma Young Boys daga Romania.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: