Abdulrazak Yahuza Jere" />

Gaskiyar Abin Da Ya Faru Game Da Dawowar ‘Yan Nijeriya 67 Daga Abidjan – NIS

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Muhammad Babandede, ya bayar da umurnin a fayyace gaskiya da kuma bukatar gyara wani rahoton karya da wata jarida ta wallafa game da dawowar wasu ‘yan kasa daga waje da aka ce hukumar ba ta yi aikinta ba lokacin da suka iso cikin kasa, a ranar Lahadi 5 ga watan Afirilun 2020.

Alhali kuma su mutanen da ake magana a kai, sun iso ne ranar Larabar nan 8 ga watan Afirilu, su 67.

Shugaban Hukumar Babandede ya nemi a rika binciko sahihin abin da ya faru wajen bayar da rahotanni musamman na abubuwa da al’umma za su yi imani da su a matsayin na gaskiya, domin wancan rahoto da aka wallafa ya cusa fargaba da damuwa a zukatan ‘yan asalin jihohin da abin ya shafa.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in yada labaran hukumar ta NIS, DCI Sunday James, ta yi bayanin cewa, “domin fayyace asalin abin da ya faru, akwai ‘Yan Nijeriya 67 da suka dawo daga Abidjan a ranar Larabar nan 8 ga watan Afrilun 2020 ta Mashigin Kasa na Seme inda Jami’an NIS suka karbe su tare da mika su ga Gwamnatin Jihar Legas bisa wakilcin mai taimaka wa gwamnan jihar na musamman a kan sha’anin kiwon lafiya, Dafta Tunde Ajayi, bayan an dauki bayanansu. Daga cikin adadinsu akwai ‘yan asalin Jihar Osun 58, na Legas 4, na Oyo 2, na Ondo 1, na Edo 1, na Ogun 1, wanda idan aka hada jimillarsu za su zama su 67 suka dawo gida”.

Shugaban NIS Babandede ya bayar da shawarar cewa a rika yin kwakkwaran bincike kan irin wadannan manyan batutuwa da suka shafi kasa tare da tabbatarwa kafin a kai ga wallafawa, kana ya tabbatar wa da ‘Yan Nijeriya irin dukufar da hukumar ta yi na kare muradun kasa a kowane lokaci.

Exit mobile version