Gaskiyar Abinda Ya Faru Tsakanin Mataimakin Gwamnan Da ’Yan Fashi A Nasarawa

A ranar Talata shekaranjiya ne da yammaci ranar, tawagar Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Dakta Emmanuel Agbadu Akabe, ta yi arangama da zugar wasu ’yan fashi da makami bayan tawagar ta bar garin Lafia ta nufi Abuja da niyyar zuwa rantsar da ministoci da za a yi jiya Laraba.

Tawagar ta isa garin Nasarawar Eggon Lafiya ba tare da tangarda ba a lokacin da su ka haura wannan tsauni da ke gab da kauyen Meni Hagon, su ka yi gamo da taron jama’a, inda a ka shaida mu su lamarin da ke faruwa a hanya.

Duk da cewa, cikin jama’ar da su ka sanar da Mataimakin Gwamnan akwai ma’aikacin fadar gwamnatin jihar wanda ya ce, a kan hanyata ta zuwa Abuja na iso daidai wannan kauyen sai a ka tsayar da ni, na ga wani mai babbar mota kirar Jeep ya sha da kyar.

Lokacin da ya ke tsaye sai ga shugaban karamar Hukumar Lafia su ma za su wuce na sanar da su ga abinda ke faruwa, kuma yawan mutanen za su kai 100 ko fiye da haka.

Bayan sanar da mataimakin gwamnan halin da a ke ciki ne, sai jami’an tsaron su ka bukaci shi da ya sassauta tafiya, su kuma za su je su kori ’yan fashin, don a samar da hanya.

 Jami’an tsaron sun yi amafani da jiniya ta saman motarsu da nufin tsorata mutanen. A kan hanyar tafiyarsu ba tare da sanin hakikanin wajen da ’yan fashin su ke ba su ka fada tarkon ’yan fashin. Nan take ’yan fashin su ka yi mu su dirar mikiya, su ka kashe mutum hudu; ’yan sanda uku da direbansu daya.

Duk da cewa, tsakaninsu da motar mataimakin gwamnan babu tazara sosai, ko da su ka ji harbe-harbe sun kaure, babu dadewa sai su ka ji shiru, kamar an yi ruwa an dauke.

A lokaci guda su ka neme su ta na’urar sadarwar motar, amma ba su ji komai ba daga jami’an tsaron. Hakan ya sanya su ka yanke shawarar karasawa zuwa wajen.

A lokacin da su ke tafiya a hankali sai jami’an tsaron DSS su ka bukaci motar Mataimakin Gwamnan ta dawo tsakiya, tasu ta shige gaba sakamakon motar da ke jan gaban ta tafi kuma ba ta dawo ba.

A lokacin da su ke tafiya sun hangi wani mutum daya a tsaye da bindiga da kakin ’yan sanda. Wannan ya sanya kokwanto a tsakaninsu su na tunanin cikin jami’an tsaronsu ne, amma me ya sa su na kiran su ba su ji maganarsu ba? Sannan  a lokaci guda mutumin da ya ke tsaye da bindigar ya na kiran su da su karaso ya na yi mu su alama da hannu cewa su zo. Wannan ya sanya DSS su ka jarraba harbi, domin tabbatar da ko waye.

Harbin da su ka yi ke da wuya sai ta ko’ina a ka kaure da harbe-harben manyan bindigogi, ashe ’yan fashin sun karkasu ne, wanda hakan ya sanya tawagar Mataimakin Gwamnan da ma sauran al’umma da su ka biyo su su ka kasance a tsakiyar ’yan fashin.

An yi ta harbe-harbe tsakanin tawagar Mataimakin Gwamnan da ’yan fashin, amma sakamakon yawan ’yan fashin ya sanya a ka fi karfin tawagar mataimakin gwamnan.

Duk da irin harbe-harbe ba tare da sassautawa ba, Mataimakin Gwamnan ya tsira lafiya sakamokon hikimar da jami’an DSS su ka yi na fitar da shi daga ainihin motarsa su ka yi ta ja da ruf-da-ciki da shi har su ka  nemi gudunmawar wata mota kirar Golf su ka saka shi ba tare da ’yan fashin sun gano su ba, su ka sulale.

Saboda karar harbe-harbe da ta kaure a dajin, al’umma da su ka biyo tawagar mataimakin gwamnan domin wucewa su na kowa ya yi ta kansa, inda a ka rika yin tafiyar kura da hadawa da jan ciki a daji.

Mutane sun gudu sun bar motocinsu a daji, kamar yadda tawagar motocin mataimakin gwamnan su ka bar nasu.

Duk da cewa, mataimakin gwamnan ba ya tafiya da jami’an tsaro sosai kwata-kwata jami’an tsaron ba su wuce tara ba masu makami. Ganau sun shaida cewa, adadin ’yan fashin za su kai 100 sanye da kakin soja da ’yan sanda.

’Yan fashin sun kashe wani direban smota kirar Sharon mai suna Sani, mutumin garin Keffi.

Da ya ke jawabi a taron jami’an tsaro, Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule, ya ce, “mu na fuskantar matsalar tsaro a cikin jiharmu, kuma  mun sha yin magana; abu ne ya ki ci ya ki cinyewa. Duk da matakan da mu ke dauka kama daga matsalar ’yan bindiga da sauransu. Yau ga shi ya faru da tawagar Mataimakin Gwamnan tsakanin Akwanga da Nasarawar Eggon.

“Idan ’yan fashi za su iya tsayawa su yi arangama da tawagar mataimakin gwamnan har su kashe ’yan sanda su kwashe makamansu, ina kuma ga sauran al’umma?

“Wannan babbar hanya ne da ba ta rabuwa da al’umma, amma a ce tsiraru su na kokarin takurawa jama’a su hana su wucewa, saboda biyan bukatarsu.

“Gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba, za ta tabbatar ta kara daukar matakai na maganace afkuwar irin wannan nan gaba. Za mu nemi taimakon gwamnatin tarayya, saboda a dauki duk matakin da za a dauka wajen kawo karshen wanan ayyukan ta’addanci.

“Ba za mu kyale batagari su na takurawa al’umman jihar Nasarawa ba, saboda idan mutane su ka bar jiharsu ta haihuwa, ina z asu je? Mu na jajentawa wadanda su ka mutu; ’yan sanda uku da fararen hula biyu.”

Shi ma a nasa jawabin, Kwamishinan ’yan sandan jihar Nasarawa, Mista Bola Emmanuel Longe, ya ce, “tabbas ba mu ji dadin faruwan wannan lamari ba, kuma abu ne wanda dole mu tashi tsaye, saboda idan a ka zura ido, ba a san inda zai tsaya ba. Mu na neman hadin kan al’ummar jihar, su ba mu goyon baya wajen bayyana ma na duk wani batagari da su ka sani.”

Lamarin dai ya faru ne ranar Talata da misalin karfe 6:25 na yammacin ranar. Cikin ’yan sandan da su ka rasa rayukansu akwai Kwamandan tafiye-tafiye Samuel, Sunday Audu, Pana, sai kuma direban da ya tuka su mai suna Adamu Audu da direban Sharon, wanda ba a cikin tawagar ya ke ba mai suna Sani.

A binciken da wakilin LEADERSHIP A YAU ya gidanar, ya jiyo ra’ayin mutane, inda su ka bayyana sakacin da a ke samu a gurin gwamnatin jihar Nasarawa, saboda zargin ba su tafiya da isassun jami’an tsaro, sabanin yadda wasu gwamnonin jihohin ke yi.

Bayan da kura ta lafa, an je an kwaso gawarwakin ’yan sanda da motoci, amma ba a ga bindigoginsu ba.

Bayan gabatar da taron kan tsaron Gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya kira jirgin ’yan sanda mai saukar ungulu, inda wata majiya ta bayyana cewa ya hau zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Nasarawa, ASP Usman Samaila ya tabbatar da aukuwar lamarin a garin Lafia.

Samaila ya shaida cewar kwamishinan jihar Bola Longe ya kafa kwamitin gaggawa da za su binciko musabbin lamarin da yayin asarar da a ka yi, hatta shi kanshi kwamishinan da mataimakinsa sun garzawa wurin da abun ya faru nan take domin binciko lamarin.

Tawagar ‘yan fashin sun bude wutar ne tun kafin tawagar mataimakin gwamnan su ankara da shirinsu, lamarin da ya janyo har suka iya illata su haka.

A fadin jami’n hulda da jama’a na ‘yan sandan, wasu jami’an ‘yan sanda uku da wani direba an harbe su har lahira suka mutu a sakamakon wannan harin na ‘yan fashi, yana mai cewar an kwashe gawarwakin zuwa dakin adana garwarwaki da ke asibitin Dalhatu Araf Specialist Hospital Lafia.

Exit mobile version