Sakamakon yanayin matsin tattalin arziki wacce cutar Korona da kuma halin da ‘yan Nijeriya suke ciki ne ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude wasu daga cikin iyakokin kasar nan, in ji wata majiya daga fadar gwamnati. Majiyar ta bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya bayar da umurnin a bude iyakokin kasar nan guda hudu saboda a rage wahalhalun da ‘yan Nijeriya da kuma ‘yan kasuwa masu zaman kansu suka shiga sakamakon rufe iyakokin kasa. Majiyar ta kara da cewa, gwamnatin shugaban kasa Buhari ta bayyana wa sauran kasashe makwabtan ba za ta lamunta da shigowa da duk wani kayayyakin wanda ba su dace ba.
Majiyar ta ce, rahoton kwamitin shugaban kasa shi ya bukaci a sake bude iyakokin kasar nan, domin a samu damar gudamar da ayyukan tattalin arziki wanda zai rage kunci da takura da ‘yan Nijeriya suka shiga sakamakon rufe iyakokin kasar nan. Rahoton ya bayyana cewa, daya daga cikin dalilan da ya sa aka bude iyakokin dai shi ne, samun damar gudanar da harkokin kasuwanci a cikin Nijeriya.
Tun a ranar 20 ga watan Agustan shekarar 2019, gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin kasar nan, domin kar a dunga shigo da makamai da wasu kayayyaki da gwamnati ta hana a shigo da su. Wannan mataki ya kara haddasa rashin ayyukan yi domin harkokin kasuwanci da dama sun sami matsaloli sakamakon daukan wannan mataki da gwamnati ta yi.
Kwamitin shugaban kasa wacce ministan kudi da kasafi da tsare-tsaren kasa, Mista Zainab Ahmad ta jagoranta, kwamitin ya bayar da cikakken baya ni, inda yake cewa, duk da matsalolin da aka fuskanta na rufe iyakokin an samu alfanu mai yawan gaske, domin ya taimaka wajen rage ayyukan fasa kwauri da fashin bakin iyakoki da sauran muyagun ayyuka da ake aikatawa. Kwamitin ya bayar da shawara ga Nijeriya wajen samar da shirin tattalin arziki da samar da tsaro da yadda masu zuba jari za su sami natsuwa.