Imam Murtadha" />

Gaskiyar Magana A Kan Maja Sirdin Mai Martaba Sarkin Kano

 ’Yan uwa na masu daraja, wasu miyagun mutane, da wasu miyagun ‘yan jaridu, kamar kamfanin jaridar The Nation da ire-irenta da wasu makiya gaskiya, ‘yan bani-na-iya, ‘yan a-bi-yarima-a-sha-kida su na ta kokarin yada labarin karya, labarin shirme, cewa wai Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya tube Maja Sirdin Sarki daga mukaminsa, wai saboda ya tarbi Gwamna Ganduje na jihar Kano, wanda sam wannan labari karya ne, sannan kuma ba haka lamarin ya ke ba. Kawai wadannan mutane su na son gyaran miyarsu ne tare da kokarin faranta ran iyayen gidansu, kamar yadda na yi bayani a rubutun da ya gabata.

Da farko, abinda ya kamata mutane su fahimta shi ne, a duk lokacin da a ke kokarin kashe wutar rikici tsakanin wasu mutane, musamman shugabanni, to za ka tarar akwai wasu mutane, ‘yan kanzagi, da basa so a sasanta, ba domin komai ba kuwa, sai domin amfanuwa da suke yi da wannan rikicin. Su a wurin su, a samu dawwamammen zaman lafiya, to toshewar hanyar cin abincin su ne yazo. Don haka za su yi dukkan mai yiwuwa wurin ganin cewa sam ba’ayi sulhu ba.

Wallahi, Allah shi ne shaida, rikicin Maja Sirdin Sarkin Kano sam ba shi da alaka da siyasa ko maganar tarben Gwamna Ganduje. Amma irin wadannan miyagun mutane masu ci da wutar rikici, su ka juya al’amarin zuwa hakan, domin su wawantar da wadanda basu gane ba, su kuma su cimma burin su da suke son cimmawa. Amma alhamdulillahi, ni da dukkanin wani mutum iri na, mai kaunar ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a Jihar Kano, da ma arewa baki daya, mun san cewa, da yardar Allah, wadannan mutane ba za su samu nasara ba.

Kamar yadda na tabbatar maku a rubutun jiya, kun san na ce sam karya ne ba a kori Maja Sirdin Sarki ba, kawai dai an karbi makullan dakin sirada ne daga hannun sa aka bai wa Shamaki nauyin amanar siradan, kafin a kammala bincike, saboda laifin da ya aikata, na barin Sirdin Sarki ya je hannun wani, ba tare da izinin Sarki ba, wanda wannan sam ba shi da wata alaka da siyasa ko tarbon Gwamna Ganduje. Sannan kuma idan ba rashin adalci irin na dan Adam ba, ai tarbon gwamna din ba shine kadai yayi ba, akwai Turakin Danrimi, shima ya tarbi gwamna Ganduje, amma me aka yi masa? Kuma sannan shi Maja Sirdin ai har yanzu shine Maja Sirdi, amma kamar yadda muka sani ne, ka’idar gidan sarautar Kano ita ce, idan aka fara satar siradan Sarki, ko kuma aka ga Sirdin Sarki a hannun wani wanda ba bashi aka yi ba, to tube su ma ake yi. Kuma shi a lokacin da aka nada shi Maja Sirdi, shin ba wani Maja Sirdin ne Marigayi Sarki Ado Bayero ya tube ba, saboda rashin kula da sirada ko satar su? Shi wannan ma ai an yi masa adalci da ba’a tube shi gaba daya ba.

Sannan kuma idan ba’a manta ba, sarautar Maja Sirdi da ma ai sarautar gidan Shamaki ce. Shamakin Kano kuma shine ya karbi makullan dakin siradan, don yana binciken yadda aka yi Sirdin Sarki ya fita, ya shiga hannun wani ba da iznin Sarkin ba.

Sannan shi ma a lokacin da aka nada shi Maja Sirdi ai Sarki Ado ne ya tube Maja Sirdi Dan Azumi Figini a matsayin Maja Sirdin sa, saboda Sirdi ya bata. Amma me yasa a wancan lokacin ba’a ce siyasa ce ba? Sai yanzu, don kawai ana son kullawa Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II sharri? Kawai mutane sun zama marasa imani da tsoron Allah a cikin al’amurran su, koda yaushe da Mai Martaba Sarki yayi wani abun da zai kara martaba da ci gaban masarautar Kano, sai kawai a nemi siyasantar da lamarin? Wace irin al’ummah ce wannan muke rayuwa a cikin ta don Allah?

Wallahi ya kamata mutane mu ji tsoron Allah, mu zama masu son kashe wutar rikici, kar mu zama masu kokarin ruruta ta. Mu sani, duk abunda muka fada ko muka rubuta, ko muka yada, to Allah yana sane da shi, kuma zai tambaye mu a kan sa gobe al-kiyama. Kar mu yarda shaidan la’ananne ya yaudare mu, yasa mu manta da cewa akwai mutuwa da hisabi.

Sannan a halin da muke ciki yanzu, musamman a arewa, akwai bukatar mu zauna lafiya da junan mu, mu hada kai, domin zaman lafiyar yankin mu da ci gaban sa.

Sannan ya kamata mu sani, ita daukaka da matsayi, Allah ne yake bayar da shi ga wanda yaso daga cikin bayin sa. Idan Allah ya daukaka mutum, ko Allah yayi masa wata baiwa ko sutura, ko Allah ya kaddari cewa shi mai mutunci ne, to kar ka taba yarda shaidan ya rude ka, kace zaka ci mutuncin mai mutunci. Yin haka zai sa ka jawo wa kanka fushin Allah Subhanahu wa Ta’ala, domin kana so ka nuna cewa Allah bai iya ba kenan da ya bashi. Sannan ina mai shawartar mu da cewa, kar mu yarda muyi hassadar duk wani mutum da Allah yayi wa wata baiwa ko daukaka a cikin al’ummah. Domin idan mun lura, hassada ita ce ke sa wasu suna yin abunda suke yi. Wasu kuwa kwadayi ne da neman abun duniya a wurin masu mulki ko ‘yan siyasa.

Sannan mutane su sani, zagi da cin mutunci da karya da kazafi da kage, duk ba za su taba yin wani tasiri a kaina ba, domin mun saba. Ba irin abun da ba ace dani ba, Amma sam ban damu ba, domin mun yi wa Allah Subhanahu wa Ta’ala alkawarin zamu kare gaskwiya kuma za mu fade ta komai dacin ta. Kuma a wurin kare gaskiyar nan ko fadar ta, bamu damu ba, ko da zamu sadaukar da rayukan mu ne, babu wani damuwa, domin ba a kan mu ne aka fara ba!

Wasu su zage ni, wai saboda ni ba dan Jihar Kano ba ne. Wai ina ruwana da harkar Kanawa. Wasu kuwa suna fada man maganganu na wulakanci da raini, wai suna cewa ina ruwana da maganar Sarkin Kano, alhali shi dan darikar tijjaniyyah ne, ni kuma ba dan tijjaniyyah ba. Duk wadannan mutane sun manta da cewa, kare martabar masarautar Kano kare addinin Musulunci ne da Musulmai, sannan kuma sun manta cewa, kare martabar arewa ne da ‘yan arewa bakidaya!

Sannan ina kira, don Allah, mu zama masu girmama Sarakunan mu, domin wallahi matsayin su, su jagororin addini ne. Idan muka yarda aka wulakanta su ko aka zubar masu da mutunci, wallahi kanmu mu ka yi wa. Allah yasa mu gane, amin.

Daga karshe, Ina mai kira da nasiha zuwa ga manyan mu na arewa, tun daga kan Mai girma shugaban kasa, Muhammadu Buhari, har zuwa gwamnonin Jihohi, da sauran su, muna jiranku mu ji abinda za ku ce da irin matakin da za ku dauka, a kan batun ‘ya ‘yan mu, ‘yan asalin Jihar Kano da a ka sace, aka kai su garuruwan inyamurai, a ka canja masu suna, kuma aka canza masu addini. Muna nan muna kallo tare da sauraron ku a kan wannan badakala, a matsayin ku na shugabanninmu!

Domin a gaskiya ya zama wajibi aji muryoyin manyan arewa da kungiyoyin arewa a wannan badakala ta satar yaran arewa da ake kaiwa Anambra da sauran jihohin inyamurai ana sayarwa, kuma a canja masu addini. Sam bai kamata mu ji shiru ba, kamar an aiki bawa garin su, ko kamar maye ya ci shirwa!

Shin ina manyan kungiyoyi da sauran kananan kungiyoyi masu ihu da tayar da jijiyar wuya a lokacin siyasa? Kada mu zama taron tsintsiya ba shara fa!

Nagode,

Dan uwanku Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto ne daga Okene ta Jihar Kogi a Najeriya. Za a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.

Exit mobile version