Idris Umar" />

Gaskiyar Maganar Kashe Wani Matashi A Garin Samaru

Daga Idris Umar, Zariya

A cikin satin da ya gabata ne wani matashi mai suna Abubakar Aliyu ya rasa rayuwarsa a sakamakon wata mamaya da gamayyar jami’an tsaro suka kai wani dandalin da ake zargin ta ‘yan shaye-shaye ce a garin Samaru karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Abubakar dan shekaru akalla 25 ne kuma bincike ya nuna cewa, ya rasa ransa ne sakamakon  wata fafara da gamayyar jami’an tsaro suka kai da suka hada da ‘yan sanda da ‘yan banga da ‘yan Zamda na shiyyar garin Samaru.

Hakan yasa Abubakar ya yi gudun fitar hankali da yasa har ya fadi sauran abokansa kuma suma suka shafa tare da samun nasara kubuta daga mamayar gamayyar jami’an tsaron.

Bayan da gamayyar jami’an tsaron sun kama Abubakar ne da kwana daya sai labari ya fara yawo a gari cewa ‘yan banga sun kashe Abubakar sakamakon duka da suka yi masa.

Hakan yasa iyayen Abubakar suka tuntubi ‘yan sanda do jin gaskiyar jitajitar dake yawo a gari na mutuwar dansu Abubakar nan ne ‘yan sanda suka tabbatar ma da iyayen Abubakar cewa tabbas ya rasu sakamakon ya yi gudun daya fi karfinsa hakan yasa suka kai shi asibiti cikin gaggawa amma daga bisani an tabbatar da cewa ya rasu.

Tuni ‘yan sanda suka aiko da gawar Abubakar gidansu dan yin masa jana’iza.

Bayan kammala jana’izan ne abokansa da ake zargin ‘yan shaye-shaye ne suka tabka wata zanga-zanga mai zafin gaske tare da kona duk wani ofishin ‘yan banga na garin Samaru baki daya.

Wakilinmu ya zanta da uban Abubakar mai suna Alhaji Musa Aliyu a kan lamarin inda ya ce, a gaskiya yaji radaddn mutuwar Abubakar amma ya bar komi ga Allah kuma ya yi matukar bakin cikin abin da matasa suka yi na kone-kone don haka don mai kaukar doka a hannunsa to bamu tare da shi kuma wadanda suka rasa kaddaransu Allah ya basu wanda yafi na da.

Hajiya Balaraba Musa marikiyar Abubakar ita ma ta koka da rasuwarsa tare da jan kunnen matasa da suka guji daukar doka a hannunsu.

Malam Dalladi Musa shi ne sarkin wannan waje ya tabbatar da kona ofishin ‘yan bangar da wasu gidaje dake kusa da ofishin ‘yan bangan sai dai ya ja hankalin matasa da su guji daukar doka a hannunsu.

Wakilinmu ya tuntubi jami’an hrulda da jama’a na rundunar ‘yansandar jihar Kaduna ASP  Mukhtar ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya musunta zargin da ake yi wa gamayyar jami’an tsaro na kashe matashin, ya na mai cewa, tsananin gudun da Abubakar ya yi ne kuma gashi ya yi mu’amula da kwayoyi hakan ta yi sanadiyyar rasa ransa. Ya kuma bayyana cewa, iyayensa sun yafe, an kuma kabi takardar da suka rubuta na yafewar a ofishin ‘yan sanda na Samaru, ya kara da cewa, yanzu haka an kama mutane 6 daga ciki wandanda suka ja ragamar tada hargtsin kuma suna ci gaba da bincike a kan lamarin.

 

Exit mobile version