Shugaban karamar Hukumar Kunchi Alhaji Aminu Idi Shuwaki ya bayyana aniyarsa na Sake fasalin Yadda aiki ke gudana a karamar Hukumar ta Kunchi, musamman batun zuwa aiki akan lokaci. Yace hankali na ya tashi kwarai da gaske ganin halin da sakatariyar karamar Hukumar Kunchi ke ciki. Wannan tasa yau Lahadi muka hallara a sakatariyar karamar Hukumar domin gudanar da aikin tsaftace sakatariyar.
Shugaban na wannan jawabi ne alokacin aikin tsaftace sakatariyar inda shugaban ya tabbatar da aniyarsa na sake fasalin tsarin gudanar da ayyuka da kuma tabbatar da ganin kowa na zuwa bakin aiki. “Ba zan amince da fashin zuwa aiki ba, kuma zamu sa kafar wando daya da duk wanda ke kokarin kassara mana aniyar mu ta sabunta fasalin karamar Hukumar Kunchi.
Alhaji Aminu Idi Shuwaki ya ci gaba da cewa, zan yi aiki tare da duk wanda zai taimaka mana wajen aiwatar da sabon salon Jagorancin da wannan Shugabanci zai ci gaba da aiwatarwa. Zamu tabbatar da inganta harkar samar da kudaden shiga, wanda hakan zai bamu damar kwararawa a al’ummar Kunchi ayyukan raya kasa.
Aminu Shuwaki yace ina da kyakkyawan yakinin kansilolina suna sane da halin da wannan karamar Hukuma ke ciki, kuma mun shigo da kyakkyawar niyya wanda ina tabbatarwa da al’ummar Kunchi ba zamu basu kunya ba. Saboda haka sai shugaban ya bukaci hadin kan jama’a, musamman Malamai da Sarakuna iyayen kasa.
Idan ba a manta ba mako biyu da suka gabata Wakilin Jaridar LEADERSHIP Ayau ya yi tattaki kafa da kafa har zuwa karamar Hukumar ta Kunchi inda muka dan tsakuro kadan daga cikin Matsalolin dake addabar yankin, musamman halin da sakatariyar karamar Hukumar Kunchi wanda wakilin leadership Ayau ta ji ta bakin wani wanda ya bukaci a sakaya sunansa, wanda ya koka bisa yadda ake kwashe wata guda ba tare da bude sakatariyar karamar Hukumar ba.
Yanzu abinda ake jira a gani shi ne yadda ma’aikatan karamar Hukumar Kunchi ke yin kunnen kashi da batun zuwa wurin aiki, sannan Suma masu rike da madafun ikon wadanda ake zargin na yin fuskar shanu wajen kin kwana a yankin.