Ilimi shine gishirin rayuwa, ya kan zama fitila mai haske ga maishi ya kuma yaye duhu na jahilci domin gyara da inganta rayuwa. A koda yaushe idan za’ayi abu matukar anyi shi cikin ilimi sannan kuma yadda kamata tabbas za’a ga nasarori da dama. Jahilci da ilimi basu kasancewa wuri daya. A duk lokacin da aka samu ilimi to ya kan kore jahilci.
Rayuwa ta mai ilimi da wanda baidashi daban ne domin kuwa, mai ilimi yana samun cigaba a fannoni daban daban na rayuwarsa saboda a duk lokacin dazai yi abu a rayuwarsa yakan sa abunda ya sani wajen yinsa. A yayinda ake samun sa6anin hakan ga wanda baida shi
Kasancewar muhimmancin da yake dashi a rayuwar mutane shi yasa hukumomi a kawacce ƙasa suke iya ƙokararinsu suga sun samar ma yan ƙasar su ingatattacen ilimi domin cigaban mutane wanda zaikawo bunkasar tattalin arziki ta hanyar dogaro da kai da walwala da kuma magance manya da kananan laifuffuka.
Duk ƙasar da kaga taci gaba to lallai zakaga tayi tanadi na musamman akan ilimantar da yan kasar. Hukumominsu sun kashe makudan kudade na samar da ilimi.
Yawancin kasashen afrika an barsu a baya wurin samar da ingatattacen ilimi ga mutanensu.
Yayinda da hukumomin kasashen Turai, Amurka, Japan, Chana, Isra’ila da sauransu suke zuba kudade wajen binkiciken kimiya da fasaha. Hukumomi a kasashen Afrika suna karkatar da kudaden ne ta hanyar daba tadace ba.
Yawancn kudin ana kashe ma yan siyasa ne sannan ma’aikatan gwamnati su sace sauran kudaden da aka ware domin yima yan kasa ayyukan cigaba.
Duk da ikirarin da ake yi na cewa hukumar ilimi da al’adu na majalisar dinkin duniya ta ware wa gwamnatoci adadin daza su kashe na kassafin kudaden su akan ilimi. A wani jawabi da yayi da manema labarai a shekarar 2017 ministan ilimi na Nijeriya Malam Adamu Adamu yace hakan ba gaskiya bane.
A lokacin, yace sati uku da suka wuce ya jagoranci jami’an Nijeriya zuwa hukumar, a lokacin an kawo maganar inda hukumar ta musanta cewa bata ta6a ware wani adadi daya kamata yan kasashe su kashe ba akan ilimi. Saboda haka maganar da ake na cewa kowacce kasa ta kashe Kashi 26 daga cikin 100 na kasafinta a harkar ilimi ba gaskiya bane. Amma dai ministan ya roki gwamnatin Muhammadu Buhari data dunga kashe Naira Tiriliyan Daya (1 Trillion) duk shekara akan ilimi.
Duk da haka kasashen Afurka musamman Nijeriya tana daya daga cikin kasashen da suke kashe kudi mafi karanci a harkar ilimi.
Tun dawowar mulkin dimukuradiya a shekarar 1999 kudin da kasar take kashewa a kan ilimi bai ya tsaya ne tsananin kashi 4 zuwa kashi 10.
Yayinda sauran kasashe masu tasowa tsararrakun Nijeriya, ba wata kasa da take kashe kudi kasa da kashi 20 wa ilimi a cikin kudin kasafinta. kasashen sun hada da Brazil, Bangaladesh, China, Egypt, India, Indonesia, Medico, Nigeria da Pakistan. Lallai a cikin kasashen da suke yammancin Sahara Nijeriya an bar Nijeriya a baya sosai wajen kashen kudi a harkar ilimi inji Minista.
A wani bincike an gano cewa daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2018 yanayin yanda Nijeriya tayi kasafin kudi a harkar ilimi ya samu tagomashi sosai. Shekarar da ilimi yafi samu kaso mai tsoka itace shekarar 2014 inda aka ware kashi 10% na kasafin shekarar akan harkar ilimi.
Duk da karanchin kulawa da fannin ilimi yake samu a wajen hukumomi wanda haka yayi sanadiyar samun komabayar ilimin sosai.
Rashin tsaro da talauci sun taimaka sosai wajen kara ruguza harkar ilimi, musamman a Arewancin Nijeriya.
A satin da yawuce yan bindiga sun shiga Makarantar Sakandare na maza dake garin Kankara Jahar Katsina inda suka sace yara sama da 600 suka tsere dasu cikin daji.daga baya an samu labarin sauran yaran kimamin kamar 200 sun gudu daga hannun maharan.
Hakan kuma ya faru ne a lokacin da Shugaban Kasa yaje jihar domin yin hutun kwanaki bakawai. Tuni dai hukumomi suka bazama neman yaran yayinda suke bama iyayen yaran tabbacin cewa yaran nan bada jimawa zasu dawo dasu gida cikin koshin lafiya. Har dai zuwa lokacin danake wannan rubuta yaran suna can hannun maharan ba’a sako suba.
Tuni dai gwamnatin Jahar Katsina da sauran gwamnatocin dake arewacin Nijeriya suka bada sanarwar rufe makarantun dake fadin jahohinsu sai Baba ta gani.
Duba ga yadda lamarin harkar tsaro kullum kara ta6ar6arewa take musamman Arewancin Nijeriya. kuma babu wata alama nan kusa da yake nuna karewar matsalar, duk da ikirarin da hukumomi suke.
Hakan na nuna cewa makomar ilimi a wannan yanki namu tasa ta kare. A lokacin da muke kokari muga mun kamo kudanci a lokacin kuma abu yake kara lalacewa.
Wannan matsalar tsaron zata hassada wa yara da yawa barin makarantu. A lokacin da muke kokarin muga yara sama da miliyan 12 da basa zuwa makaranta a arewa an kai su.
Yanzu dai ya rage ga hukumomi da shuwagabannin alumma da sarakuna dana addini da yan kasuwa da yan boko da kungiyoyin matasa na wannan yanki su tashi tsaya haikan domin yakar wannan babban bala’i na rashin tsaro da yake neman ya durkusar damu.
Bayan haka mutane su fito su matsama hukumomi domin ganin an samu tabbtaccen sauyi akan ilimin dazai amfani alumma. Allah yayi mana jagora Amin.