GDPn Kasar Sin Ya Karu Da 8.1% Zuwa Yuan Tiriliyan 114 A Shekarar 2021

Daga CRI Hausa,

 

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta sanar Litinin din cewa, Jimillar GDPn kasar ya zarce Yuan triliyan 110 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 17.3, yayin da aka samu karuwar kashi 8.1 cikin 100 zuwa yuan tiriliyan 114.367, kwatankwacin US dala tiriliyan 17.6 a cikin shekarar 2021.

Alkaluma sun nuna cewa, yawan karuwar da masana’antun kasar suka samu, wani muhimmin ma’aunin tattalin arziki, ya karu da kashi 9.6 bisa dari a shekarar 2021. Yayin da adadin kadarorin kasar ya karu da kashi 4.9 a shekarar 2021.

Shi ma jarin kaddarori na kasar ya karu da kashi 4.9 bisa dari a shekarar 2021. Haka ma yadda ake zuba jari a fannin raya kadarori, ya karu da kashi 4.4 cikin dari a bara idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Rahoton hukumar kididdigar kasar ta Sin ya nuna cewa, yawan marasa aikin yi a biranen kasar, ya kai kashi 5.1 bisa dari, kasa da kashi 0.5 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. (Ibrahim Yaya)

Exit mobile version