A cikin wannan watan da muke ciki ne hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasar Libaria ta bayyana sunan tsohon dan ƙwallon ƙafar ƙasar, George Weah, a matsayin wanda yalashe zaben shugaban cin ƙasar da akayi a satin daya gabata.
Wannan dai ba shine karo na biyu da Weah yake tsayawa takarar ba inda ko a shekarun baya ya tsaya takarar sai dai yasha kasha a hannun shugabar ƙasar ta yanzu, Ellen Johnson Sirleaf wadda taci zaben a karo na biyu a lokacin.
Tun bayan kammala yaƙin basasa a ƙasar, a shekara ta 2005 George Weah ya yanke shawarar tsunduma harkokin siyasa domin bada gudunmawa wajen gina ƙasar ta Libaria sai dai yasha suka daga bangarori daban-daban na ƙasar inda aka dinga zarginsa da rashin cikakken ilimi da ƙwarewa wajen mulkar al’umma da kuma rashin sanin siyasa.
Shugabar ƙasar ta wannan lokaci, Ellen Johnson Sirleaf ta zargi Weah da rashin sanin matsalolin yan ƙasa da kuma rashin sanin abinda yakamata yayi idan an zabeshi a matsayin shugaban ƙasa.
Har ila yau, an zargi Weah da yataba zama dan ƙasar faransa a lokacin da yake buga ƙwallo a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint German a shekarar 1992 zuwa 1995 wanda hakan yaja cecekuce a ƙasar kuma hukumar zabe ta ƙasar ta wanke shi kuma tabashi damar tsayawa takarar shugabancin ƙasar a shekarar ta 2005.
Weah yayi takarar shugabancin ƙasar a shekarar 2005 sai dai yasha kayi a hannun Sirleaf din bayan anyi zagaye na biyu a zaben inda ta lashe zaben da kashi 59.4% cikin dari yayinda shi kuma yasamu ƙuri’a kasha 40.9% wanda hakan yabata damar lashe zaben.
Sai dai bayan sanar da sakamakon zaben George Weah yayi allah wadai da sakamakon inda yace zaben cike yake da magudi da rashin adalci kuma magoya bayansa sunyi zanga-zanga a babban birnin ƙasar na Manrobia kafin daga bisani su haƙura.
Shugabannin ƙasashen Africa da dama sunyi kira ga Weah daya karbi sakamakon zaben cikin ruwan sanyi domin kaucewa wani sabon yaƙin basasar kuma hukumar hadin kan ƙasashen Africa ta ayyana zaben a matsayin cikakken zabe kuma karbabbe.
Rashin ilimin Weah yaja akacigaba da sukarsa a siyasar ƙasar ta Libaria sai dai yataba cewa “Duk masu ilimin da suka mulki ƙasar basu tsinanawa ƙasar komai ba” a wata hira da yayi da manema labarai a lokacin da aka tambayeshi akan maganar rashin cikakken ilimin nasa.
Tsohon dan wasan yayi karatun digiri a makarantar Parkwood dake birnin landan a fannin kula da wasanni sannan yayi karatun diploma a fannin kasuwanci a jami’ar DeɓRy dake jihar Miami dake ƙasar amurka.
Yaci gaba da bada gudunmawa a siyasar ƙasar Libaria inda a shekarar 2009 ya tsaya takarar sanata a ƙarƙashin jam’iyyar Congress for Democratic Change kuma ya lashe zaben inda yazama sanata mai wakiltar arewacin ƙasar.
A shekarar 2016 ne ya sake bayyana aniyarsa ta sake takarar shugabancin ƙasar inda ya fuskanci mataimakiyar Sirleaf Josep Boakai kuma ya samu nasara bayan da akaje karo na biyu a zaben da aka gudanar a wannan watan da muke ciki.
George Weah dai shine dan wasa na farko a duniya daya taba zama shugaban ƙasa a duniya kuma wannan ba ƙaramin tarihi bane a harkar siyasar duniya, Africa dama libaria gaba daya.
Ta Yaya Za A Yi Mulkin?
Wannan itace tambayar da zatazo kan kowa domin ansan cewa Weah dai dan wasane kuma ƙwararre amma yashiga siyasa kuma yazama shugaban ƙasa a ƙasa kamar libaria wadda tayi fama da yaƙe-yaƙen basasa.
A baya yasha suka a hannun yan adawa sosai inda suka dinga cewa baisan yadda ake mulki ba kuma bashi da ilimi sosai na yadda zai tafiyar da al’umar ƙasar ta libaria.
Sai dai tun farko yanada goyon bayan musamman samarin ƙasar domin suna ganin tunda tsohon dan ƙwallo ne kuma yanada sha’awar shigar da matasa cikin gwamnati kamar za’a samu canji a ƙasar.
George Weah dai shine dan Africa na farko a duniya wanda yataba lashe kyautar dan wasan dayafi kowanne dan wasa iya ƙwallo a duniya a shekarar 1996 a lokacin yana buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AC Millan ta ƙasar italiya.
Har ila yau a shekarar ne yazama dan wasan dayafi fice a nahiyar turai da nahiyar Africa da ƙasar libaria kuma ya zura ƙwallaye da dama a shekarar.
Har yanzu dai a Africa babu dan wasan da yayi abinda Weah yayi na nuna irin wannan bajinta kuma ya lashe ktyaututtuka daban-daban a duniya kafin yayi ritaya daga buga ƙwallo.
A tarihinsa ya bugawa ƙungiyoyi irinsu MIGHTY BARROLE, INƁINCIBLE ELEƁEN, AFRICA SPORTS, TONNERRE YOUNDE, MONACO, PSG, AC.MILLAN, CHELSEA, MANCHESTER CITY, MARSEILLE DA ALJAZIRA kafin yayi ritaya yakoma siyasa.
Sannan yaci ƙwallaye 134 cikin wasanni 350 daya buga a duniya sai dai bait aba zuwa ya buga gasar cin kofin duniya ba a tarihi domin ƙasarsa bata taba zuwa ba kuma wannan abun shine kadai ya tsayawa George Weah a rayuwarsa inda yace yana baƙin cikin hakan.