Abba Ibrahim Wada" />

Gerard Pique Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Sipaniya Wasa

Dan wasan baya na Barcelona Gerard Pique ya yanke shawarar daina bugawa kasarsa ta Sipaniya  (Spain) kwallo bayan shafe shekaru tara yana wakiltar kasar a wasanni daban daban na duniya.

Gerard Pique mai shekaru 31 ya yanke hukuncin domin ya samu damar mayar da hankali kan buga wasa a kungiyarsa ta Barcelona sannan kuma yana bukatar hutu a cewarsa a shafinsa na yanar gizo.

Wannan hukunci nasa na zuwa ne duk da an nada tsohon mai horas da Barcelona Luis Enrique a matsayin sabon wanda zai jagoranci kasar ta Sipaniya bayan kammala gasar cin kofin duniyar da aka kammala.

Pique dai yana cikin wad anda suka taimakawa kasar Sipaniya ta samu nasarar lashe gasar cin kofin Duniya kimanin shekaru takwas da suka gabata, da kuma kofin nahiyar turai a shakara ta 2012.

Amma sai dai rashin tabuka wani katabus a gasar kofin Duniyar da ya gabata a kasar Rasha 2018, ya sanya ya shi sake tunani ga kuma shekaru na cimmasa, don haka ya ga ya kamata ya matsa yara su dana.

Exit mobile version