Connect with us

LABARAI

Gezawa 2019: Alhaji Ahmad ‘Edplorer’ Ya Shirya Wa Kansiloli Shan Ruwa

Published

on

A shekaran jiya ne shahararren dan kasuwa, kuma jigo a siyasar Jihar Kano, Alhaji Ahmad Hasan Gumawa, wanda aka fi sani da lakabin ‘Edplorer’ ya shirya shan ruwa na musamman ga Kansilolin mazabar Gezawa da Gabasawa ta Jihar Kano.

Liyafar shan ruwan ya samu halartar Kansiloli 11 da ake da su a Gezawa.

An gudanar da liyafar shan ruwan ne a gonar Honorabul Ahmad ‘Edplorer’ da take garin Gunduwa a Gezawa.

Wannan taron liyafar shan ruwa an shirya shi ne don karfafa alaka tsakanin masu ruwa da tsaki a Mazabar ta Gezawa da Gabasawa.

Kansilolin da suka halarta sun nuna jin dadinsu da irin wannan karramawa da Hon. Ahmad (Edplorer) ya yi musu. Sannan kuma sun yi fatan Allah ya gabato da zaben 2019 don al’ummar wannan mazaba su yi wa ‘Edplorer’ ruwan kuri’u.

Yayin da yake jawabi a wurin taron, Alhaji Ahmad Hassan ‘Edplorer’ ya bayyana farin ciki da yadda Kansilolin suka amsa gayyatarsa. Ya ce; “Wannan ya nuna Kansilolinmu na tare da mu. Kuma insha’Allah ba za mu ba su kunya ba wurin hidimtawa al’ummar wannan yanki na Gezawa da Gabasawa.”

Alhaji Ahmad ya ci gaba da bayyana irin tulin kudurorin da yake da su ga al’ummar wannan mazaba, wanda kuma yake sa ran aiwatar da su a aikace idan Allah ya ba shi ikon darewa kan kujerar
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: