Ghali Na’abba  Ga Buhari: Ka Manta Da Batun Sake Yin Takara

Tsohon Kakakin Majalisar wakilai, Ghali Na’abba, ya ce, shi bai ga wani abin da Shugaba Buhari, ya tsinanawa kasarnan ba, har da zai ce zai sake tsayawa takarar neman Shugabantar ta.

A wani taro na masu fada aji, na Jam’iyyar APC, Shugaba Buhari, ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan karo na biyu a 2019.

Shugaban ya ce,  ya yanke shawarar tsayawa takarar nebisa yawan kiraye-kirayen da ‘yan Nijeriya ke yi ma shi na ya sake tsayawa takarar a karo na biyu, domin ya ci gaba da ayyuka masu kyau da ya faro.

Sai dai, mutane da yawa sun soki wannan shawarar da Buhari ya yanke, inda suka yi nu ni da gazawarsa kan yakan rashawa da cin hanci kamar yadda ya alkawarta lokacin neman zabensa.

Cikin wata tattaunawa da ya yi da Jaridar ‘Sunday Newspaper,’ Ghali Na’abba, cewa ya yi, shi bai san abin da ya baiwa Shugaba Buhari karfin gwiwar sake tsayawa takarar ba.

Na’abba, ya shawarci Shugaba Buhari, da ya sake tunani kan shawarar na shi, duk da cewa ba mu yi mamakin hakan ba, amma mun tabbata ba abin da zai iya tabukawa.”

“Tabbas, a matsayinsa na Shugaba mai ci, zai iya amfani da karfin mulkin sa domin ya sake darewa kujerar mulkin, amma gaskiyan magana, duk wanda ya aikata kamar na shi, bai kamata ya shugabanci Nijeriya ba.

Da aka yi ma shi tambaya, kan furucin da Obasanjo ya yi, na cewa, APC da PDP, ba za su iya ceto Nijeriya ba, Ghali Na’abba, ya amsa da cewa, “Na yarda da shi kan hakan, amma dubi da yanayin siyasar kasarnan, kana tunanin sabbin Shugabannin da kake magana, za su iya karban Shugabanci daga ‘yan mazan jiyan, kasantuwar karfin da suke da shi, ba su kuma shirya barin mulkin ba?

“Har yanzun ‘yan Nijeriya suna nan inda suke, wannan lokacin jarabawa ce ga ‘yan Nijeriya. Ina da tabbacin wannan karon za su tagaza wajen zaban shugabannin da suka cancanta da za su iya biyan masu bukatun su, na tabbata komai na iya faruwa a 2019.

“Tsoro na kawai, kar  a samar da shugabannin da za su kara raba Nijeriya. A yanzun haka Nijeriya a rabe take, ba kuma za mu so a kara kawo rarraba a cikin ta ba. Neman mafita muke yi yanzun, muna neman wanda zai yi gyara ne.”

 

Exit mobile version