Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Gibin Dake Tsakanin Masu Kudi Da Talakawa Ya Haifar Da Karuwar Matsalolin Da Suke Shafar Kare Hakkin Bil-Adama A Amurka

Published

on

Kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin ta kaddamar da wani rahoto mai lakabin “Gibin dake tsakanin masu kudi da talakawa ya haifar da karuwar matsalolin da suke shafar kare hakkin bil-Adama a kasar Amurka”, inda ta tono yadda ake kara samun gibin dake tsakanin masu kudi da talakawa a Amurka, duk da Amurka na da karfin tattalin arziki da wadata. Karuwar bambancin da ke tsakanin masu kudi da talakawa a gida ta haddasa rashin adalci a tsakanin al’ummar Amurka ta fuskar tattalin arziki. Talakawan suna kara fuskantar matsalolin zaman rayuwa, yayin da ake kara samun matsalolin da suka shafi kare hakkin bil-Adama.

Rahoton ya jaddada cewa, kusan rabin magidanta Amurkawa ba su iya rayuwa yadda ya kamata. Matsalar kangin talauci ta haifar da lalacewar tsarin kiwon lafiyar al’ummar Amurka. Wadanda ba su da inshorar lafiya sakamakon kangin talauci ba su iya biyan kudin samun jiyya. Matsakaicin tsawon rayukan mutane ya ragu yayin da yawan wadanda suke kashe kansu ya karu a Amurka.
Dangane da dalilin da ya haifar da bambancin da ke tsakanin masu kudi da talakawa, rahoton ya nuna cewa, tsarin dimokuradiyyar Amurka ya kau da kai daga hakkin jama’a a fannonin tattalin arziki, zaman al’ummar kasa da al’adu, lamarin da ya kara gibin da ke tsakanin masu kudi da talakawa. Kana gwamnatin Amurka ba ta so a daidaita lamarin, maimakon haka, sai ta dauki wasu matakai da manufofi, wadanda suka tsananta halin da ake ciki a kasar. Abubuwan da suke faruwa a kasar ta Amurka suna da nasaba da tsarin siyasarta da kuma manyan masu ra’ayin jarin hujja da gwamnatin ke wakilta. Harkokin siyasa da suka kara dogaro da kudi sun sanya gwamnatin Amurka ta zama kakakin masu kudi.
Bayanin ya yi karin bayani da cewa, gibin da ke tsakanin masu kudi da talakawa a Amurka ya dade yana kasancewa a kasar. Ba za a iya sauyawa cikin gajeren lokaci ba. Illolin da za a haifar kan hakkin jama’ar Amurka za su tsananta a kwana a tashi. (Mai Fassarawa: Tasallah Yuan)
Advertisement

labarai