Gidajen Adana Namun Daji 8 Mafi Girma A Duniya

Idan muka yi la’akari da gidan Zoo na Red McCombs Wildlife da ke Tedas mai girman kadada 12,000 za a iya dauka shi ne mafi girman gidan zoo a duniya. kuma yana da nau’ikan dabbobi iri daban-daban har 20, sannan shi ne gidan zoo da aka fi bai wa namun daji kulawa.

Duba da shirin wadannan gidan zoo da irin dabbobin da ke ciki ya sa aka fara tunanin shin wane gidan adana dabbobin daji ne mafi girma a duniya.

1. Gidan Zoo na Henry Doorly Zoo
Nebraska, na farko kenan da masu sha’awar kallo ke biyan kudi, Gidan Zoo na Henry Doorly a Omaha yana dauke da kusan dabbobi 17,000 da nau’insu ya kai 962. Yana da fadin fili da ya kai kadada 130 a yankin. Ko da yake akwai manyan gidajen namun daji a yankin amma duk da haka ba su kai girman gidan Zoo na Henry Doorly idan duka wadannan nau’ikan an hada su.

A saboda wannan dalili ne aka sanya shi a matsayin daya daga cikin manyan gidajen zoo mafi girma a duniya. Hakanan an tabbatar da shi ne katafare kuma hadadden gidan Zoo mafi girma a Arewacin Amurka, kuma
mai dauke fadama ta cikin gidan mafi girma a duniya.

2. Gidan Zoo na Berlin
An bude gidan namun daji na Berlin a cikin shekara 1844, Lambun Zoological na Berlin (Zoologischer Garten Berlin) shi ne mafi tsufa kuma sanannen gidan zoo a Jamus. Fadin filinsa ya kai girman kadada 84, kuma yana cikin Tiergarten na Berlin. Yana dauke da nau’ikan dabbobi 1,500 daban-daban da yawan nau’in ya kai 17,000. Shahararrun namun dajin dake gidan sun hada da Bao Bao, Giant Panda da Knut polar bear, amma kuma (Knut din ya mutu ba zato ba tsammani a cikin Maris 2011).

3. Gidan Zoo na Beijing

An kafa gidan Zoo na Beijing shi a shekara 1906 a lokacin daular king, gidan namun daji na Beijing yana da tarin dabbobi mafi girma a kasar Sin. Gidan namun daji yana da dabbobi 14,500, kuma akwai nau’ikan dabbobi sama da 450 da fiye da nau’ikan dabbobin ruwa 500. Gidan namun dajin yana da girman kadada 219. Gidan Zoo na Beijing tabbas an fi saninshi da tarin dabbobin da ba a saba gani ba a kasar China ciki har da Giant Pandas, wadanda su ne shahararrun wuraren shakatawa.

4. Gidan Zoo na Brond
Gidan Zoo na Brond dake birnin New York, an bude shi a cikin shekarar1899, kuma shi ne babban gidan namun daji a Amurka, wanda ya ke girman da ya kai kadada 265, da kuma fadin filin shakatawa da ya kai fadin murabba’i 107. Gidan namun dajin yana dauke da dabbobi sama da 4,000 da nau’insu ya kai 650.

5. Gidan Zoo na Toronto
An gina shi a Toronto yana da fili da ya kai girman kadada 71. Gidan Zoo na Toronto shi ne gidan zoo mafi girma a Kanada. Gidan yanzu yana dauke dabbobi sama da 16,000, nau’insu ya kai 491. An raba dabbobin zuwa yankuna bakwai da suka hada da: Indo-Malaya, Afirka, Amurka, Tundra Trek, Australasia, Eurasia da kuma yankin Kanada.

  1. Gidan Zoo na San Diego
    Gidan Zoo na San Diego yana daya daga cikin shahararrun gidan namun daji a duniya yana da dabbobi sama da 4,000 da nau’insu ya kai 800. Yana da girman kadada 100 tare da filin shakatawa, yana nan a Birnin San Diego.
    Yanayin ruwan teku na Kudancin California ya dace da yanayin dabbobi wadanda ke rayuwa a wurin.

7. Gidan Zoo na Moscow
An bude wannan gidan Zoo ne domin baki masu zuwa yawon bude ido, tun daga shekarar 1864. Gidan namun dajin na Moscow yana daya daga cikin tsofaffin gidajen adana namun daji a Turai. A yau, gidan namun daji na Moscow yana da dabbobi sama da 6,000, kuma akwai namun daji sama da 927, kuma yana da girman kusan kadada 53, wanda shi ne babban gidan zoo a kasar Rasha.

  1. Gidan adana namun daji na Columbus din na Arewacin Columbus, Ohio. Wato ‘Columbus Zoo,’ gida ne da ke dauke da dabbobi sama da 5,000, kuma yana cike da nau’ika sama da 700 da aka rarraba su zuwa wasu yankuna na duniya.
    A shekara ta 2004 gidan namun dajin ya fara aiki don fadada gidan zuwa girman kadada 82 a cikin shekaru 10 masu zuwa. Daga nan kuma an yi nufin fadada shi zuwa kadada 120 don ya dace da yanayin muhallin sabanna na Afirka.
Exit mobile version