Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home ADABI

Gidan Dabino: Gwarzonmu Na Wannan Mako

by Tayo Adelaja
October 1, 2017
in ADABI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Bango majinginar marubuta shi ne taken da ya dace da Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino, MON; shahararren marubucin littattafan Hausa ne a Arewacin Nijeriya, mai shiryawa da bayar da umarni ne a shirin finafinan Hausa, sannan ya na fitowa a matsayin dan wasa kuma dan jarida.

Ranar Juma’ar da ta gabata 29 ga Satumba, 2017 ta zo daidai da cika shekara uku da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bai wa Gidan Dabino lambar yabo ta MON. don haka mu ka ga ya dace zame ma na gwarzon wannan mako, domin na baya su amfana da irin hikimomin da ke cikin nasarorinsa a rayuwa.

Ado Ahmad Jajirtacce ne kuma uba wanda duk wani abu da ya shafi marubuci da harkar rubutu zai tsaya sai inda karfinsa ya kare.Ado ba shi da kasala ko ganda a jikinsa da aljihunsa a kan duk abinda ya shafi Adabi musamman a bangaren rubutaccen adabi. Duk wanda zai budi baki in dai kan Alh Ado ne to shakka babu alheri zai furta.Rayuwa irin ta Ado ita ce abar koyi ga na gaba don samun nagartattun matasa.

Haihuwarsa Da Fadi Tashinsa Na Neman Ilimi

An haife shi a shekara ta 1964 a garin danbagina da ke karamar Hukumar Dawakin Kudu. Ya girma a Unguwar Zangon Barebari a cikin birnin Kano. Ya fara karatun allo, (Alkur’ani) a makarantar marigayi Malam Rabi’u a Unguwar Zangon Barebari, a shekarar 1968 da karatun littattafai na Islamiyya a makarantar marigayi Sheikh Tijjani na ‘Yanmota, (1971).

Bai sami damar yin karatun boko yana karami ba, sai da ya girma sannan ya shiga makarantar ilmin manya ta Masallaci Adult Ebening Classes, Kano a shekara ta 1984 zuwa 1986. Ya yi makarantar sakandare ta dare (G.S.S. Warure Ebening Session), Kano a shekara ta 1987 zuwa 1990. Ya shiga Jami’ar Bayero inda ya sami takardar shaidar Diflomar kwarewa a kan ya]a labarai, wato (Professional Diploma in Mass Communication) a Sashen Koyar da Aikin Jarida, a shekara ta 2004 zuwa 2005.

Shigarsa Duniyar Adabi

Ya rubuta littattafai da aka buga su kamar haka: In Da So Da kauna 1-2 da Masoyan Zamani 1-2 da Hattara Dai Masoya 1-2 da Wani Hani Ga Allah 1-2 da Duniya Sai Sannu da Kaico! da Malam Zalimu (wasan kwaikwayo) da Ina Mafita (wasan kwaikwayo) da Dakika Talatin (wasan kwaikwayo) da Mata Da Shaye-Sayen Kayan Maye: Ina Mafita? da Sarkin Ban Kano, Alhaji Dr. Muktar Adnan (tarihi), wanda suka rubuta tare da Sani Yusuf Ayagi da From Oral Literature to Bideo: The Case of Hausa. (Takardun da suka gabatar a jami’a Hamburg, Jamus, shi da Farfesa Abdalla Uba Adamu).

An kuma fassara wasu daga cikin littattafansa guda uku daga harshen Hausa zuwa Turanci: The Soul of My Heart (Fassarar In Da So Da kauna) da Nemesis (Fassarar Masoyan Zamani) da kuma Kaico! (Fassarar Kaico!) Young Women Substance Abuse and The Way Out (Fassarar Mata Da Shaye-Sayen Kayan Maye: Ina Mafita?)

Ya gabatar da mukalu da dama a tarurrukan kara wa juna sani a cikin Nijeriya da kasashen waje. Wasu daga cikin takardun nasa an buga su a cikin kundaye (littattafai). Yana yin rubuce-rubuce a cikin jaridu da mujjalun Hausa.

Tare da shi aka kafa wasu kungiyoy, kamar kungiyar Marubuta ta Nijeriya Reshen jihar Kano, (ANA) a shekara ta 1992, kuma ya rike shugabancinta na tsawon shekara uku da kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kano, (Kano State Filmmakers Association) wanda a halin yanzu shi ne shugaban riko na kungiyar da kungiyar Marubuta ta Raina Kama (Raina Kama Writers Association) wanda kuma shi ne shugabanta.

Shi ne Mai Gabatar da shirin Alkalami Ya Fi Takobi, a gidan rediyo Freedom, Kano da kuma shirin Duniyar Masoya a gidan rediyo Shukura FM da ke Damagaram, kasar Nijar.

Harkar rubuce-rubuce da kuma wallafa ta ba shi damar zuwa kasashe fiye da goma sha biyar na Afrika, sannan kuma a kasashen Turai ya sami zuwa London da France da Italy da kuma Germany.

Ya zama zakaran gasar rubutun wasan kwaikwayo ta shekarar 2009 ta tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir karaye, a Abuja, Nijeriya.

Ya sami takardun yabo da dama daga jami’o’i da kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da gwamnati, saboda gudummawa iri-iri da yake bayarwa wa]anda suka shafi harshen Hausa da adabi da al’adu ta fannin rubuce-rubuce da shirin finafinai da aikin jarida da harkokin kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da kuma gwamnati. A ranar 24 ga watan Nuwamba na shekarar 2011 ya sami takardar yabo daga Inuwar Jama’ar Kano, (Kano Forum) cikin mutane goma sha ]aya da aka yaba da su a jihar Kano wajen bayar da gudummawa game da ci gaban al’umma.

Sannan a ranar 29 ga watan Satumba na shekarar 2014, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama shi da lambar yabo ta kasa mai taken, Member of the Order of the Niger (MON) bisa hidimta wa jama’a da yake yi a cikin ayyukansa.

Yana cikin wasu kungiyoyi kamar haka: Motion Picture Practitioner’s Association of Nigeria, (MOPPAN) da Association for Promoting Nigerian Languages and Culture, (APNILAC) da West African Research Association (WARA) da Indigenous Languages Writers Association of Nigeria (ILWAN) da sauransu.Mutum ne mai sha’awar tafiye-tafiye da rubuce-rubuce da bincike-bincike. Yana da mata ]aya da ’ya’ya biyar.

Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shi ne Shugaba kuma Daraktan Gudanarwa na kamfanin. Gidan Dabino International Nigeria Limited.

Littattafan Marubuci

In da so da kauna, 1, 2 (1991)

Hattara Dai Masoya, 1, 2 (1992)

Masoyan Zamani, 1, 2 (1993)

The Soul of my Heart, (Fassarar In da so, 1993)

Wani Hanin ga Allah…, 1, 2 (1994)

Nemesis, (Fassarar Masoyan Zamani, 1995)

Kaico!, (Hausa, 1996)

Duniya Sai Sannu!, (1997)

Sarkin Ban Kano, Alhaji Dr. Muktar Adnan

(Ado Ahmad da Sani Yusuf Ayagi, 2004)

Malam Zalimu, (Hausa, 2009)

From Oral Literature to Bideo: The Case of Hausa,

(Ed: Joseph Mclntyre and Mechthild Reh, 2011 )

Mata da Shaye-Shayen Kayan Maye: Ina Mafita?, (2012)

Dakika Talatin, (2015)

Littattafai Masu Fitowa

Ina Mafita?

Kaico! (Fassara zuwa Ingilishi)

Young Women Substance Abuse and The Way Out

(Fassarar Mata da Shaye-Sayen Kayan Maye: Ina Mafita?)

Malam Zalimu (Fassara zuwa Ingilishi)

 

Mene Ne Alfaharinsa?

Ina Alfahari na samun nasarori da yawa,

  1. Sunana a fagen rubutun Hausa ya je inda har duniya ta tashi ba zan je ba.
  2. Mutane manya da kanana suna son su hadu da ni mu gaisa har mu yi huldar arzki.
  3. Samun takardun yabo daga wurare daban-daban a gida Nijeriya, musammna babbar da ta fi ko wace girma wato ta MON Member of the Order of the Niger

Kalubalen da ka Fuskanta

Dalubele kullum a cikinsa nake musamman a tsakanin masu harkar rubutu da harkar fim, wasu in ka taimake su daga baya su ne masu ci maka dunduniya. Wasu kuma suna ganin don me ma ka zama yadda kake a yanzu, ba su san irin fadi tashi da gwagwarmayar da ka yi ba har ka zo wannan matsayin. Wani mawaki Aminu Abubakar Ladan ALA ya na cewa, jajircewa ita ce turbar nasara. Ga abin da baitukan wakar Shahara su ke cewa:

Zahiran dukkan ni’ima za ta sha hassada da kuna,

Kowa ka gani a inuwa tambaya ya sha fa rana,

Wanda ya yi barci na rana ba shi cara ko a ina,

Masu minshari saleba ba su zamtowa kamana,

Masu hikima sun bayani mai bidar shara da suna.

Ba shi barci ko ya huta lokaci na dare da rana,

An ka ce yaro gulamu bata dare ka yi suna

In ko ka ki kuwa ka zamto mai kamar kumfa sanina,

Ko kamar gishiri na andir ya yi fuuu haka sai ya kwana,

Ka zama tamka da iska mai kadawa ko a ina

Burinsa

Burina ina gama da duniya lafiya in kuma cika da imani, zuri’ar da na bari Allah ya shirya min su ya sa su zama wadanda za a tuna da su da kyawawan ayyukan da suka yi, kamar yadda nake fatan ni ma za a tuna da ni bayan raina.

 

Kiransa Ga Marubuta Da Makaranta

Ina kira da marubuta su yi rubutu mai ma’ana, su kula da addininsu da al’adarsu a duk abin da za su yi.

Su kuma makaranta su dinga kokarin karanta rubuce rubucen da za su karu da su ba na sharholiya kawai ba. Kuma su dinga ga bai wa marubuta shawara in sun ga kurakurai a cikin littattafansu

Allah ya hada kan marubuta, ya kare su daga shaidanun ciki.

Mun gode kwarai

Ni ma na gode, Allah ya yi wa wannan sabuwar tafiyar ta wannan jaridar LEADERSHIP A YAU LAHADI albarka, amin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Mene Ne Adabin Kasuwa? (III)

Next Post

Mutuwar Aure A Yau, Wa Ke Da Alhaki?

RelatedPosts

Rubutu

Shiga Tsakanina Da Masoyina Ya Sa Na Fara Rubutu – Na’eemerh Sulaiman

by Muhammad
1 day ago
0

Fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa, wacce ke sharafinta a yanar gizo...

Irin Ilimin Da Muka Karu Da Shi A Gidan Dambe Saboda Fim Din Gidan Dambe – Marubuta

Irin Ilimin Da Muka Karu Da Shi A Gidan Dambe Saboda Fim Din Gidan Dambe – Marubuta

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Daga Maje El-Hajeej Hotoro, Kano A makon da ya gabata,...

TSARABAR RAMADAN: Rubutacciyar Waka Daga Abdulhamid Maluman Matazu

TSARABAR RAMADAN: Rubutacciyar Waka Daga Abdulhamid Maluman Matazu

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Gabatowar watan Ramadan, wanda al'ummar musulmi ke azumtar dukkan ranakun...

Next Post

Mutuwar Aure A Yau, Wa Ke Da Alhaki?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version