Daga Sagir Abubakar, Katsina
Hukumar gudanarwar gidan rediyon Jihar Katsina ta bayyana shirinta na taimaka wa duk wata hukuma ko kungiya domin fadakar da al’umma a kan ayyukanta. Shugaban gidan rediyon Alhaji Sani Bala Kabomo, ya bayyana haka a lokacin da ya amshi bakunci jama’ar hukumar kula da lafiya daga tushe kwanan nan a ofishinsa.
Alhaji Sani Bala Kabomo da ya samu wakilcin daraktan shirye-shirye na gidan rediyon Kabir Abdullahi Abasaya ya ce, gidan rediyon na gudanar da shirye-shiryen kiwon lafiya da ke da nufin fadakar da kan al’umma a kan harkokin kiwon lafiya.
Sai dai shugaban gidan rediyon ya ce, cikakken gangamin fadakarwa ta hanyar kafafen yada labarai da sauran hukumomin da suka kamata, ita ce hanya mafi sauki ta shawo kan harkokin kiwon lafiya da suka shafi kananan yara.
Dakata Shema’u ta bayyana gidan rediyon a kan ci gaba da wayar da kan al’umma a kan harkokin kiwon lafiya ta hanyar tallace-tallace, bugo waya da sauraronsu domin fadakar da al’umma.
Haka nan ta ce, gwamnati ta yi kokari sosai game da kulawa da kafafen yada labaru tun ba yau ba dukkanin kafafen yada labaran da ke jihar suna amfana da shirin gwamnati hatta ma kafafen yada labarai na kasashen duniya da na cikin gida ba kamar wannan lokacin a wannan gwamnatin ta Gwamna Aminu Bello Masari gwamnatin Jihar Katsina ta samu jangwarzon shugaba kuma haziki.