Ibrahim Muhammad" />

Gidauniyar Ado Bayero Ta Gudanar Da Taro A Kan Rikicin Manoma da Makiyaya

Gidauniyar Ado Bayero karkashin jagorancin Alhaji Abdullahi Ado Bayero ta gudanar da  taron lakca karo na hudu na tunawa da marigayi Sarkin Kano Alhaji Dkt. Ado Bayaro taron da aka gudanar a dakin taro na cibiyar nazarin dimokwaradiyya ta Malam Aminu Kano da kafi sani da MAMBAYYA  a yammacin  ranar Asabar.

Da yake gabatarda lakca a kan abubuwa da suke faruwa dake jawo rashin jituwa tsakanin makiyayay da manoma Dakta Aliyu Salisu Malami a jami’ar Bayero ta Kano ya yi dogon bayani akan musabbabinda ke jawo rikicin ya kuma danganta ci gaban rikicin da ake da cewa rashin lurane daga Gwamnati wajen daukar matakin da ya dace da za a maganta lamarin.

Dokta Aliyu ya kawo misali da cewa makiyaya an mamaye musu burtalai da inda suke kiwo da inda shanunsu suke shan ruwa ba tare da samar musu da yanda za su yi kuma dole su samawa dabbobinsu abinci.Yayi nuni da cewa yin adalci a tsarin shi ne kawai zai iya kawo karshen lamarin da yake jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Dokta Aliyu Ya yi nuni da cewa a kwai kasashen duniya da idan kaje baza kaga shanu na yawo a gari ba, amma suna da wadatar madarar amma a nan kasar akwai shanu ko’ina amma ana karancin madara. Idan aka samar da tsari ga makiyaya za a iya cimma irin wannan nasara a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasar arziki da ake samu daga shanu wanda yafi na tsirrai da ake shukawa yawa.

Shi ma a nasa jawabin kwamishina a ma’aikatar harkokin cikin gida Alhaji Ado Ja’afar wanda ya wakilci Ministan harkokin  cikin gida Janar mai ritaya Abdulrahman Bello Danbazau  ya gode wa gidauniya bisa shirya wannan taro na lakca  dan tattauna wannan al’amari mai muhimmanci dan a samo bakin zaren da za’a warware matsalar rikicin Fulani da Manoma da yake dada kamari a kasarnan.

Tun da farko a jawabinsa na maraba shugaban Gidauniya na tunawa da marigayyi Ado Bayero. Wanda daya daga cikin ya’yane gare shi Alhaji Abdullahi Ado Bayero ya ce, makasudin wannan taron lakca wanda shine karo na Hudu ana yine dan tunawa da marigayi sarkin kano da irin gudummuwa daya bayar ta kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da cigaban al’umma .

Yace dan haka aka zabi ayi lakcar  akan rigingimu dake faruwa tsakanin manoma da makiyaya dan tattauna hanyoyinda  za’abi a sami daidaita lamarin  dan haka sukasa abin ya zama na tattaunawa  da  masana da masu neman ilimi da sauran bangarorin al’umma  kowa ya bada tasa gudummuwar  ta yanda  za’a warware matsalar.

Alhaji Abdullahi Ado yace ya tabbatar da mai martaba sarkin kano Alhaji Ado Bayero yana raye  zaiyi farin ciki yaga cewa  an warware matsalolin fada tsakanin manoma da makiyayay cikin nasara.Yace baya ga taron lakca gidauniyar tana ayyuka wajen tallafawa al’umma da gina makarantu,masallatai dakai dalibai makaranta  dan dorawa akan irin ayyukan marigayin wajen kyautata cigaban al’umma.

Cikin wadanda suka halarci taron akwai babban limamin Kumashi na Kasar Ghana  Sheik Yusufiyya da sauran mutane da suka hada da malaman addini dana book dalibai da sauran al’umma na bangarori  daban-daban.

Exit mobile version