Gidauniyar Bill Gates za ta samar ma masu cutar kanjamau magani mai rahusa tare da basu taimako.
Za a samarwa masu jinyar cutar kanjamau maganin cutar mai araha tare da tallafin kudi daga gidauniyar Bill Gates.
Cibiyar yaki da cutar kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ce ta sanar a ranar alhamis din makon da ya gabata cewa, gidauniyar Bill Gate ta bayar da tabbacin daukar nauyin sarrafa wani adadin maganin, yayin da kamfanonin sarrafa magungunan kuma suka amince su kayyade kudin maganin zuwa dala 75 kan kowanne majinyaci a shekara.