Idris Aliyu Daudawa" />

Gidauniyar ‘OB Lulu Briggs’ Ta Yi Wa Mata 100 Fidar Kaba Kyauta

Gidauniyar OB Lulu Briggs tare da hadin gwiwar asibitin koyarwa na jami’ar jihar Ribas da babban asibiti dake Fatakwal sun yi ma mata 100 fidar cutar kabar ciki a jihar Ribas.

Shugaban gidauniyyar Seyi Lulu Briggs ta bayyana cewar ita gidauniyyar ta yi haka ne domin tallafa wa mata talakawa dake fama da wannan ita cutar.

Ta yi kartin bayanin cewar “Gidauniyyar OB Lulu Briggs wata gidauniyya ce wanda mijina marigayi Dokta OB Lulu Briggs ya kafa domin tallafa wa mutane musamman talakawan kasarnan.

“Tun bayan rasuwar sa ne ranar 27 ga watan Disamba na shekarar data gabata, wannan shine karon farko da gidauniyyar ta fara aiki domin talakawa a kasar nan.

Seyi ta ce wannan karon gidauniyar zata yi wa mata dake fama da kabar ciki fida kyauta.

Bayan haka kuma a taron wata likita dake aiki da babban asibiti dake Fatakwal Rosemary Ogu ta bayyana cewar ya kamata a rika yawar wa mutane kai game da wannan cutar.

Ta kara da cewar ita cutar ta fi kama mata masu shekaru 35 zuwa sama da matan da suka isa haihuwa amma basu haihu ba.

“Bayannan kuma kamar dai yadda ta ci gaba da bayani “ koda anyi wa mace fidar cutar zata iya dawowa, idan har dai mace bata dauki ciki ba, bayan shekaru uku da aka yi mata fidar.

Exit mobile version