Haruna Akarada" />

Gidauniyar Ogan Boye Da Kungiyar Matasan Likitoci Sun Tallafa Wa Marasa Lafiya

Wannan aikin ya gudana ne a karamar hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano. Wakilinmu ya sami ganawa da wasu daga cikin jagororin wannan aikin. Da farko mun sami ganawa da Jamilu Attashir, wanda aka fi sani da Barista, shi ne jagoran wannan gidauniya ta Ogan boye, ya bayyana dalilin wannan aikin taimako, inda ya ce an sami hadin gwiwa ne da wasu kungiyoyi wajen guda 30 na matasan likitoci domin gudanar da wannan aikin a wannan unguwa ta mazabar kaura-goje.
Ya ce “Wannan magunguna da wannan gidauniya ta sayo sun shafi cututtuka kala-kala, kuma wanda aka auna su aka ga larurarsu babbace za mu aika su asibiti, wannan shi ne abin da muka yi. Kuma abin ya zo mana da bazata, saboda mutanen sun haura yadda muka yi zatonsu, wannan ne ya sa bamu hana kowa ba muka tsaida mutane muke basu abin da ya samu, domin mutanan sun kai mutum 2000, mu kuma mutum 1000 muka kiyasta, sannan kuma wanda za mu tura asibiti idan maganin da aka rubuta musu mai tsada ne, to Ogan boye ce za ta taimaka wannan shi ne.
Abu na biyu akwai gidan sauro da aka ce mu ba musu da shi amma da muka zo sai muka ga sun yi yawa yanzu abin da muka yi shi ne, mun dauki sunayensu amma mata masu ciki za mu ba wa wannan gidan sauro.
Fatan wannan cibiya ta taimaki al’umma kuma za mu ba da gudunmawa ko ta ina ba sai harkar lafiya ba, a’a har wajen ilimi.
Kuma muna kira ga al’umma da su ci gaba da taimakawa jama’a, Idan ana taimakawa to wata rana koken zai ragu.
A bangaern tawagar likitocin mun sami ganawa da Hussaini Abdulkadir wanda ya yi magana a madadin shugaban wannan kungiya Abdurrahman Musa Hassan,  ya ce sun zo nan a madadin likitoci sun duba marasa lafiya, kuma sun ba su magani, sun samu gudunmawa daga Alhaji Yusuf Ogan boye tare da makarrabansa, babu abinda za su ce da Allah sai godiya, dama su aikin su shi ne tallafawa al’umma.
Shi ma Usman Muhammad Ya’u wanda aka fi sani da Rochas, ya ce yana cikin kwamatin wannan aikin kuma an yi wannan ne domin a taimakawa jama’a wannan aikin dama kungiyar ta saba yi a fadin kasar nan wannan karon ne Alhaji Yusuf Ogan boye ya kawo shi wannan mazaba. Shi ma Gaddafi Hassan yana daya daga cikin masu hidima a wannan waje ya ce wannan aikin an fara shi ne tun karfe bakwai na safe amma yanzu kimanin biyar kenan ba’a gama ba. Ita kuwa Khadija Musa Sani shugabar mata ta Kwankwasiyya ta ce wannan aikin alkairi Alhaji Yusuf ne wato Ogan boye ya ba da umarnin haka.
Aisha Abubakar, daya daga cikin wanda suka amfana da wannan magani ta zo ne daga unguwar Rimin A’i, ta samu wannan magani tana mika godiya ga Alhaji Yusuf Ogan boye ta yi fatan Allah ya kara masa arziki.
Shi kuwa Ofisa ya bayyana irin aikin da suka yi a wannan waje ya ce wani aiki ne mai wahalar gaske tun da na iyaye mata ne.

Exit mobile version