Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Gidauniyar Ogan Boyen Kwankwasiyya Da “YOMPON” Sun Ba Marasa Lafiya 1,500 Magani Kyauta A Kaura Goje

by Muhammad
January 24, 2021
in LABARAI
1 min read
Boye
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Ibrahim Muhammad,

Gidauniyar Ogan Boyen Kwankwasiyya karkashin Alhaji Yusuf Imam da hadin-gwiwar Kungiyar matasa likitoci ta “YOMPON” sun gudanar da duba marasa lafiya kyauta da kuma basu magani.

samndaads

Duba marasa lafiyan da suka kunshi maza da mata yara da manya an gudanar da shi ne a filin shinge dake mazabar Kaura Goje a karamar hukumar Nasatawa ranar Asabar.

Da yake bayani ga wakilimmu akan makasudin gudanar da tsarin na duba lafiya da bada magani kyauta, shugaban gidauniyar Ogan Boye, Hon Abdullahi  Kamal Ali ya ce, shirin na jinkai ne da Gidauniyar   ta saba gudanarwa a fannoni daban-daban.

Ya ce shugaban Gidauniyar na Ogan Boye Alhaji Yusuf Imam ya sahale ayi aikin duba marasa Lafiyan da mutum sama da 1,500 suka amfana da magani kyauta.

Ya ce, likitoci guda 50 ne suka yi aikin akan kowace irin cuta  da take damun mutum, wacce ake iya bada maganinta nan take aka bayar, wanda kuma take da bukatar zuzzurfan bincike za a tura Asibiti don kulawa da marasa lafiyan a karkashin gidauniyar.

Wadanda suka amfana da wannan tagomashi na duba lafiya da basu magani kyauta sun yaba tare da godewa Alhaji Yusuf Ogan Boye bisa wannan kulawa da ya yi musu tare da yi masa addu’ar Allah ya biya mass bukatunsa.

SendShareTweetShare
Previous Post

Daga Darajar Masarautar Rano A Gwamnatin APC Nasarar Ganduje Ce -Hon Idi Gwangwan

Next Post

Gwamnatin Gombe Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da NNPC Kan Samar Da Mai Daga Tsirrai

RelatedPosts

Dan Majalisar Tarayya Ya Sabunta Katin Jam’iyyar APC A Funtuwa

Dan Majalisar Tarayya Ya Sabunta Katin Jam’iyyar APC A Funtuwa

by Muhammad
6 hours ago
0

Daga Hussaini Yero, Funtua  Dan majalisar Tarayya me wakiltar mazabar...

Sace Daliban Zamfara: Sarkin Musulmi Da Gwamna Tambuwal Sun Kai Ziyarar Jaje

Sace Daliban Zamfara: Sarkin Musulmi Da Gwamna Tambuwal Sun Kai Ziyarar Jaje

by Muhammad
6 hours ago
0

Daga Hussaini Yero, kasa da awa goma sha biyu da...

miyagun kwayoyi

Masu Garkuwa Da Mutane Muggan Kwayoyi Suke Bukata Matsayin Kudin Fansa – NDLEA

by Sulaiman Ibrahim
7 hours ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa Shugaba kuma babban jami’i na Hukumar...

Next Post
Tsirrai

Gwamnatin Gombe Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da NNPC Kan Samar Da Mai Daga Tsirrai

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version