Gidauniyar Ogan Boyen Kwankwasiyya Da “YOMPON” Sun Ba Marasa Lafiya 1,500 Magani Kyauta A Kaura Goje

Boye

Daga Ibrahim Muhammad,

Gidauniyar Ogan Boyen Kwankwasiyya karkashin Alhaji Yusuf Imam da hadin-gwiwar Kungiyar matasa likitoci ta “YOMPON” sun gudanar da duba marasa lafiya kyauta da kuma basu magani.

Duba marasa lafiyan da suka kunshi maza da mata yara da manya an gudanar da shi ne a filin shinge dake mazabar Kaura Goje a karamar hukumar Nasatawa ranar Asabar.

Da yake bayani ga wakilimmu akan makasudin gudanar da tsarin na duba lafiya da bada magani kyauta, shugaban gidauniyar Ogan Boye, Hon Abdullahi  Kamal Ali ya ce, shirin na jinkai ne da Gidauniyar   ta saba gudanarwa a fannoni daban-daban.

Ya ce, dama kungiyar matasa likitoci sun saba yin irin wannan fita dan taimakawa marasa lafiya.Dan haka suka nemi hadin gwiwa da Gidauniyar Ogan Boye domin gudanar da duba matasa lafiya a Karamar hukumar Nasarawa.

Ya ce shugaban Gidauniyar na Ogan Boye Alhaji Yusuf Imam ya sahale ayi aikin duba marasa Lafiyan da mutum sama da 1,500 suka amfana da magani kyauta.

Ya ce, likitoci guda 50 ne suka yi aikin akan kowace irin cuta  da take damun mutum, wacce ake iya bada maganinta nan take aka bayar, wanda kuma take da bukatar zuzzurfan bincike za a tura Asibiti don kulawa da marasa lafiyan a karkashin gidauniyar.

Wadanda suka amfana da wannan tagomashi na duba lafiya da basu magani kyauta sun yaba tare da godewa Alhaji Yusuf Ogan Boye bisa wannan kulawa da ya yi musu tare da yi masa addu’ar Allah ya biya mass bukatunsa.

Exit mobile version