Daga Zubairu T. M. Lawal, Lafia
Gidauniyar Sir Ahmadu Bello Sardaunar Sakkwato karkashin Jagorancin Tsohon Mai shari’a Alhaji Mamman Nasir Galadiman Katsina, ta ziyarci gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Umar Tanko Al-makura a gidan gwamnati da ke garin Lafia.
Da yake jawabi yayin ziyarar, shugaban tawagar Alhaji Mamman Nasir ya ce; “Makasudin zuwanmu shi ne hada danganataka mai karfi tsakanin wannan gidauniya da Gwamnatin Jihar Nasarawa”.
Tare da cewa; “Makasudin kafa wannan gidauniyar shi ne yadda yanzu wasu ke kokarin ganin an raba kasar nan ba tare da sun san wahalar da magabata suka sha wajen hada kasar ta zama dunkulalliyar kasa daya ba”.
Haka nan, ya ce, za su tashi tsaye su yi kira ga duk wanda yake da hakki a kasar nan da ya zo su hada kai don wayar da kan yara da kanne saboda a kan bikatar da ke akwai na a zauna tare cikin lumana. Ya ci gaba da cewa wannan shi ne dalilin da ya sanya suka soma ziyartar gwamnonin jihohi domin hada hannu a dunkule waje daya.
Shi ma da yake jawabi, Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Umar Tanko Al-makura, ya jinjina wa wannan tawagar ta Gidauniyar Sardauna, saboda yadda ta dauki matakin hada kan al’ummar kasar nan ta yadda za a fahimci juna a zauna lafiya . A A cewar gwamnan, Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello, ya yi aiki tukuru wajen ganin kan ‘yan kasa ya hade ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba.
Haka nan, ya ce Gwamnatin Jihar Nasarawa za ta hada hannu da wannan gidauniyar wajen tunawa da ayyukan Sardaunan Sakkwato, domin cinma burin samar da zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin Arewa da kasa baki daya gami da samar da matsaya guda.
Gwamna Al-makura ya ce, tun lakocin da ya kama mulkin jiharsa ba shi da wani buri wuce samar da zaman lafiya da hadin kan al’ummar. Saboda a cewarsa, wannan shi ne koyi da ayyukan alheri na marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato kuma shi ma tafarkin da kama kenan.