Muhammad Awwal Umar" />

Gidauniyar Zarah And Arthur Ta Raba Wa Dalibai Marasa Karfi Tallafi

Gidauniyar Zarah And Arthur

Gidauniyar Zarah and Arthur ta rabawa daliban makaranta ‘yan faramare ‘yayan marasa karfi su hamsin tallafin kayan karatu a karamar hukumar Chanchaga. Da ta ke bayani a wajen taron bada tallafin, ‘yan majalisar dokokin jiha mai wakiltar karamar hukumar Gurara, Hon. Binta Mamman kuma mataimakiyar shugabar masu rinjaye a majalisar dokokin Neja, ta yabawa shugabar gidauniyar Zarah and Arthur da Stars Foundation akan kokarin da ta ke yi sama da shekaru da dama wajen tallafawa marasa karfi, mata da matasa da a in hannunta wanda wannan kuduri ne mai kyau.

Hon. Binta ta jawo hankalin, Hajiya Zarah I. Abdullahi da kar ta gaji da irin wannan namijin kokarin da ta ke yi wajen tallafawa marasa karfi domin sakamakon ta na wajen Allah. Saboda haka a shirye mu ke duk wani gudunmawar da ki ke nema daga wajen mu za mu bayar dan karfafa guiwar ki a wannan tafiyar, saboda haka mu iyaye mata muna yabawa da ayyukan wannan gidauniyar.
Hajiya Zarah I. Abdullahi, ita ce shugabar gidauniyar Zarah and Arthur da Stars Foundation, tace wadannan ayyukan da wadannan gidauniyoyin ke gudanarwa ayyuka ne da ta kuduri aniyar aiwatarwa da abin hannunta, wanda koda ana samun tallafi yana fitowa ne da ‘yayan wannan kungiyoyin na ta wanda kashi tis’in cikin dari daga aljihunta ya ke fitowa.
Hajiyar tace ganin irin halin da annobar Korona ta jefa mutane ta ga dacewar fitar da wani dan tallafawa ilimin ‘yayan marasa karfi wanda a yau ta fara da yara hamsin daga karamar hukumar Chanchaga. Wanda an zakulo yara hudu daga dukkanin mazabun da ke karamar hukumar wadanda iyayen marasa karfi ne su ke cin gajiyar wannan tallafin.
Tace mun kuduri baiwa yaran tallafin littafan rubutu da karatu, jakkuna da indimie da wasu abubuwan da zasu karfafa guiwar yaran dan mayar da hankalin su kan karatu duba da irin koma bayan da wannan annobar ta janyo mana.
Yakubu Muhammad Ruga, jami’in ma’aikatar ilimi ta jiha yace wannan tallafin tamkar sanya gishiri ga nufin gwamnatin jiha na dawo da martabar ilimi ga kananan yara, domin kamar yadda shirin gidauniyar ya nuna yara ne ‘yan aji uku zuwa biyar ne zasu ci ribar tallafin wannan tamkar kwarin guiwa ne aka kara wa yaran dan mayar hankalin su akan karatu.
Da ya ke jawabi a taron, kwamishinan matasa da wasanni na jiha, Hon. Emmanuel Umar Baga, ya jawo hankalin yaran da su zama masu kula tare da biyyaya ga malaman su, musamman dan ganin sun samu nasarar cike gurbin abinda aka rasa da annobar Korona ta janyo.
Da ta ke kaddamar da shirin, babban daraktan hukumar kula da hakkin kananan yara ta jiha, Hon. Maryam Haruna Kolo,ta yabawa shugabar gidauniyar Zarah and Arthur musamman ganin a kowani lokaci hankalin ta na ga inganta rayuwar kananan yara, wanda muna fatan su ne zasu zama shugabannin gobe, dan haka mu iyaye da kungiyoyin kare hakkin kananan yara muna alfahari da ke kuma za mu cigaba da baki goyon baya a duk lokacin da ki ka bukaci hakan.
Matan shugaban karamar hukumar Bosso Hajiya Hannatu Gomna ce ta wakilci matan shugabannin kananan hukumomin Zone ‘B’ tare da wakilcin wasu kungiyoyin mata da matasa, da wakilcin jami’an tsaron NSCDC da hukumar kare hadurra ta kasa FRSC.

Exit mobile version