Ammar Muhammad" />

Gidauniyyar Sarkin Musulmi Ta Fara Rabon Abinci A Sakkwato

Gidauniyyar Sarkin Musulmi da ke yada zaman lafiya da ci gaba, a jiya Lahadi sun kaddamar da fara rabon abinci ga marayu da kuma ‘yan gudun hijirar da suke jihar Sakkwato.

Shugaban gidauniyyar, Alhaji Muhammadu Mera, wanda kuma shi ne Sarkin Argungun, a yayin da ake rabon abincin, ya ce wannan wani mataki ne na tallafawa mabukata saboda alfarmar watan Ramadan. Inda ya ce; manufar gidauniyyar shi ne tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Nijeriya, tare da kuma yaki da talauci da yunwa a tsakanin al’umma.

Ya ce sun fara kaddamar da rabon abincin ne a Sakkwato, wanda kuma za su fadada wannan aiki zuwa jihohin Kebbi da Zamfara, kuma ya ce suna fatan daga shekarar 2020, za su fadada wannan aikin zuwa wadansu jihohin kasarnan.

Malam Muhammad Maidoki, shugaban hukumar Zakka da wakafi na jihar Sakkwato, ya jinjinawa wannan shirin, inda ya bayyana cewa tabbas zai rage radadin talauci da al’umma ke fama da shi. Sannan ya ce akalla marayu 400 da ‘yan gudun hijira 50 ne za su amfana da wannan shirin, inda ya ce; kowannensu zai samu buhun shinkafa guda, da man gyada da kuma naira dubu daya. A karshe, Maidoki ya yi kira ga masu kudi da shugabanni da su yi koyi da Sultan wajen tallafawa mabukata a cikin al’umma.

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya kafa wannan gidauniyyar ne a watan Nuwamban 2014, da manufar yada manufofin zaman lafiya da hadin kai da kuma ci gaban kasa, tare da wayar da kan al’umma sakon Musulunci da kuma tallafawa mabukata a Nijeriya.

 

 

Exit mobile version